Home / News / Na Fi Kowa Cancantar Zama Shugaban APC Na Kasa – Abdul’Aziz Yari

Na Fi Kowa Cancantar Zama Shugaban APC Na Kasa – Abdul’Aziz Yari

Daga Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar dai yadda al’ummar Jihar Zamfara da ke arewacin tarayyar Najeriya ke kokarin bayyanawa duniya irin nagarta, hakuri da juriyar babban jigon siyasar Jihar da Najeriya baki daya Alhaji Dokta Abdul’Aziz Abubalar Yari Shatiman Zamfara, kasancewarsa mutumin da ke taimakawa dimbin jama’ar birni da karkara wanda hakan ya Sanya kowa ya rungume shi hannu biyu sakamakon shiga cikin zukatan jama’a.
Kamar yadda mai rubutun nan ya zagaya domin jin ta bakin jama’a game da nagartar mai neman kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa wato Dokta Abdul’Aziz Abubakar Yari, kamar yadda wani da ya zagaya cikin Jihohi ya rika yin tuntuba tsakanin jama’a domin ganin jama’ar sun fahimci kowa ye wannan bawan Allah Dokta Abdul’Aziz Abubakar Yari mai neman kujerar shugaban jam’iyyar APC da ke zaman jagoran jam’iyyu sauran na bin bayanta.
Kamar yadda muka tuntubi wanda ya jagoranci wata tawagar mutanen da suka zagaya cikin Najeriya ya shaida mana irin karbuwar da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Abul’Aziz Yari ya yi a wurin al’umma ya ce shi kansa lamarin ya bashi tsoro kwarai domin sun ga abin da ake kira farin jinin jama’a da kuma shauki¬† da zakuwa tare da dokin da wasu ke da shi na ganin lokacin zaben shugabannin APC ya zo domin burinsu ya cika Abdul’Aziz ya zama shugaban jam’iyya na kasa.
Bari in dan mayar da ku baya kadan zuwa Jihar Zamfara a can ma kamar yadda jama’a ke fadin cewa babu wani dan siyasar da ke iya daukar larurar jama’a a Jihar kamar Abdul’Aziz Yari domin shike bayar da kayan arziki kusan kowa ya shaida abin da aka yi a koda yaushe har lokacin Azumi, Sallah karama da babba da ake yin layya da kuma lokacin Damina da jama’a ke komawa Gona domin Abdul’Aziz na kokarin samawa manoma dakin Zamani ta yadda za su gudanar da Nomansu cikin sauki abinci ya wadata a kasa.
Kamar yadda muka ji babban Gwarzon na cewa “ni na fi kowa cancanta in zama shugaban jam’iyyar APC na kasa domin Allah ya ba ni ikon yi wa Jiha ta da kasa baki daya aiki kuma duk an samu nasarorin da ake bukata saboda haka ina tabbatarwa da jama’a idan suka amince Mani na zama shugaban APC zan yi iyakar bakin kokari na wajen kara kawo ci gaba ga Najeriya”.
Yari ya ci gaba da cewa “na zama sakataren jam’iyya na Jiha, na zama shugaban jam’iyya na Jihar Zamfara, na zama dan majalisar wakilai ta tarayya, na kuma yi Gwamnan Jihar Zamfara tsawon shekaru Takwas (8) wanda cikin wannan lokaci na zamana Gwamna na samu damar da Gwamnoni suka ba ni na zama shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya don haka idan an zabe ni shugaban APC na kasa za a ci gaba da ganin al’amuran ciyar da kasa gaba”.
Tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari ya kuma nuna wa Gwamnan Jihar Zamfara kauna da Dattako inda ya tara taron manema labarai tare da dukkan yayan jam’iyyar APC mutane Bakwai daga kowace karamar hukuma da ya kira taron manyan jiga Jigan yayan jam’iyyar APC ya shaidawa duniya cewa sun amince da Dawowar Gwamnan Jihar Zamfara jam’iyyar APC kuma ya halarci taron karbar Gwamnan da ya dawo APC da aka yi a babban filin wasa na garin Gusau, hakika wannan Dattako ne musamman ganin cewa babu wani mutum da a halin yanzu da ke da akalar jama’ar Jihar Zamfara da duk abin da ya ce shi za su aikata sakamakon irin rikon arzikin da yake yi masu.
Kuma kamar yadda muke ruwaito maku kwanan baya cewa da akwai dimbin nagoya bayan tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari da ke cewa su duk inda tsohon Gwamnan ya nufa can za su bi shi, akwai kuma masu cewa su na yin jam’iyyar APC ne saboda tsohon Gwamna Abdul’Aziz Abubakar Yari, don haka idan ya ce ayi Gabas, Yamma, Kudu ko Arewa can za su nufa ba wani ba ta lokaci.
Irin wadannan abubuwan da ke nuna tsabar goyon baya ga tsohon Gwamnan kuma jigo da le matsayin jagora ya sa ake ganin duk inda ya nuna goyon bayansa ga wani ko wasu Yan takara nan ne za a samu rinjaye saboda kamar yadda suke yi masa lakabi da cewa ruwan dare ne mai gama duniya kuma ruwan Jakara ne in kai baka sha ba to, wani naka ya sha, wato ma’ana dai irin yadda yake yi wa jama’a abin alkairi ya game ko’ina don haka sai Abdul’Aziz mai kokarin fitar da jama’a cikin halin kangin zamani.
Mustapha Imrana Abdullahi ne ya rubuto wannan makalar
080 3606 5909

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.