Home / News / Zamfara: Mun Amince Da Gwamna Mutawalle, A Matsayin Jagoran APC Na Zamfara, Inji Abubakar Aliyu MC Tsafe

Zamfara: Mun Amince Da Gwamna Mutawalle, A Matsayin Jagoran APC Na Zamfara, Inji Abubakar Aliyu MC Tsafe

Zamfara: Mun Amince Da Gwamna Mutawalle, A Matsayin Jagoran APC Na Zamfara, Inji Abubakar Aliyu MC Tsafe
Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Mulkin Tsafe a jahar Zamfara, Alhaji Abubakar Aliyu MC ya baiyana takaicinsa dangane da irin wasu rahotani na rashin gaskiya da haddasa rikici da suke yawo a cikin al’umma dangane da jayyayar jagorancin jam’iyyar APC a jahar Zamfara.
Inda ya baiyana cewar, duk mai ra’ayin ci gaban jahar Zamfara da jam’iyyar APC ya amince da umurnin uwar jam’iyya na hannunta jagorancinta ga Gwamnan Jahar Zamfara, Honarabul Bello Muhammadu Mutawalle ba tare da jinkiri ba.
Ya fadi haka ne a shirin ‘Turbar DIMOKARADIYYA na gidan talbijin na Liberty.
Abubakar Aliyu MC ya ce;  duk dan jam’iyyar APC a Zamfara da yake adawa da dawowa Gwamnan Bello Mutawalle a jam’iyyar, hakika ba al’umma jahar Zamfara ne a gabansa ba, illa son kai da fitina.
 Yace ba shakka akwai wasu manyan Jam’iyyar APC da suke kawo hana ruwa gudu akan nasara dawowar Gwamnan jahar Zamfara, Hon Bello Muhammadu Mutawalle a jam’iyyar APC daga PDP da cewar, wannan rashin kunya ne da son rai na wasu da suke ganin ala dole sai sun yiwa jama’a mulkin danniya da kaka-gida akan lamuran ci gaban jahar Zamfara duk da yake al’umma sun wahala da hakan a baya.
Ya baiyana duk wani mai son samuwar zaman lafiya, arziki da ci gaban al’umma a jahar Zamfara, tabbata yana murna akan wannan ci gaban da aka samu na hadewa abokan adawa a wuri daya tsakanin gwamna da yan jam’iyyar APC a dai dai lokacin da ake fuskantar barazana da karin matsalolin rashin tsaro a jahar Zamfara da wasu makwabanta.
Alhaji Abubakar Aliyu MC Tsafe ya tunatar da al’umma jahar cewar, tun farko irin wannan rashin hadin kai da fahimtar juna akan abin da ya haddasa ma jam’iyyar APC inda ta rasa dukkan kujeri na mukaman siyasa tun daga yan Majalisar jaha har zuwa na Wakilai da Sanatoci da gwamna; don haka yanzu har wasu su baiyana basu amince ba, akwai takaici da ban mamaki.
Yace, duk mutumen kirki yana son ganin anyi bakunci an samu karuwa a gidansa, wanda ya tabbatar da zuwan gwamna Bello Mutawalle da jama’arsa da zama alheri da kawo karshen tashin tashina na adawa da rudani a tsakanin gwamnati da yan adawa.
Dangane da haka ya baiyana goyon baya da biyayyarsa da sauran jama’ar da yake wakilta ga shugabanci Gwamna Bello Mutawalle tare da kira ga dukkan sauran yan jam’iyya dake da sha’awar son ci gaba da zaman lafiya dasu nuna hakan garesa.
Ya nemi gwamnan jahar Zamfara da ya kwatanta adalci tare da hada kawunan yan jam’iyya baki daya tun daga matakin runfuna har zuwa jaha.
Haka ma ya yaba da aikin da Shugaban riko na jam’iyyar APC na kasa, gwamnan jahar Yobe Malam Mai Mala Buni yayi ga kawo karshen cece kuce na shugabanci inda ya rusa jagoranci jam’iyyar daga kasa har zuwa sama.

About andiya

Check Also

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka A Bakura Da Maradun

A ci gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.