Home / News / Balarabe Musa Ya Karyata Sauka Daga Mukaminsa

Balarabe Musa Ya Karyata Sauka Daga Mukaminsa

Balarabe Musa Ya Karyata Sauka Daga Mukaminsa

Mustapha Imrana Abdullahi

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya Karyata rade radin da ake yadawa cewa wai ya sauka daga mukaminsa na kwamitin Amintattun Jam’iyyar PRP na kasa.
Kamar yadda tsohon Gwamnan Tsohuwar Jihar Kaduna ya bayyana wa manema labarai lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta KSMC a cikin shirin siyasa na bakin zaren cewa duk labarai da ake yadawa a wasu kafafen yada labarai cewa wai ya ajiye mukaminsa na shugaban kwamitin amintattun PRP cewa ba gaskiya ba ne, don haka kada mutane su amince da wannan bayanai na karya.
Ya ci gaba da cewa akwai dai matsalar batun bangaranci ne kawai wato na bangaren shi a matsayinsa na shugaban kwamitin amintattu da kuma shugaban jam’iyyar PRP.
“Kuma tun farko an samu kuskure ne da aka yi shawar cewa a bude domin yan Boko da masu hannu da shuni su shigo cikin PRP da niyyar a ciyar da ita gaba, amma sai ga shi lamarin ya zama bazata”.
Ya kara da cewa zamu kira babban taro na kasa domin a warware komai saboda a samu ciyar da jam’iyyar gaba.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.