Home / News / Bamu Da Rahoton Wani Ya Fita APC – Oshiomhole

Bamu Da Rahoton Wani Ya Fita APC – Oshiomhole

Imrana Abdullahi
Hedikwatar Jam’iyyar APC a tarayyar Nijeriya ta tabbatar da cewa ba su da wani rahoton wani ko gungun wadansu mutane sun fice daga cikin jam’iyyar APC a Jihar Edo.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga babban ofishin Jam’iyyar da ke garin Abuja inda suka ce su ba su da wani tabbaci a rubuce ko a haka nan daga wani ko wasu cewa sun fita daga APC.
Bayanin Ofishin APC ya ci gaba da cewa ba zamu yi amfani da rahotannin da ake samu daga jaridu ba cewa wasu sun fita daga jam’iyyar.
“Mu bamu da wani rahoto ko hujja a rubuce da zamu dogara da shi cewa wai wani ko wasu sun fice daga cikin APC a Jihar Edo, don haka muna jira ne mu samu rahoto”.
A safiyar yau ne Gwamnan Jihar Edo Mista Godswin Obaseki bayan ganawarsa da shugaban kasa ya bayyana ficewarsa saga cikin jam’iyyar APC kuma ya ce yana kokarin yin takarar Gwamna domin samun wa’adin mulki karo na biyu a wata jam’iyyar da bai bayyana ba.
Ita dai jam’iyyar APC na gudun kada Gwamnan Jihar Edo mai ci a yanzu Godswin Obaseki ya yi mata takara ne saboda matsalar takardun da ta ce yake da su

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.