Home / Labarai / BILIYAN 30 :ZA A GINA TITUNA A JIHAR YOBE

BILIYAN 30 :ZA A GINA TITUNA A JIHAR YOBE

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a ranar  ya amince da ware zunzurutun kudi kimanin Naira biliyan 30 domin gudanar da ayyuka daban-daban a fadin jihar da suka hada da gina Sabbin Tituna da gyara Tsoffin da suka lalace.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci taron majalisar zartarwa jihar na karshe a gwamnatinsa ta farko da aka gudanar a dakin taron zauren majalisar da ke gidan gwamnati a garin Damaturu.
Da yake karin haske ga manema labarai kan sakamakon taron zartarwa, Kwamishinan Ma’aikatar Samar da Arziki, Karfafawa da Samar da Aikin yi na Jihar, Abdullahi Bego, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya taya duk dan majalisar da ya samu damar yin aiki a majalisar zartaswar jihar fatan alheri dangane da ayyukan da suka gudanar cikin gwamnatinsa
Abdullahi Bego ya kara  bayyana cewa Buni wanda ya jagoranci zaman majalisar (Exco) na karshe a gwamnatinsa ta farko yana cike da farin ciki kan aiyyukan da ‘yan majalisar zartaswar suka yi a shekaru hudu da suka gabata.
Ya kuma yi nuni da cewa gwamnan ya ji dadi sosai da majalisar kwamishinoninsa bisa irin gudumawar da suka bayar na kai-da-kai da kuma hadin-gwiwarsu ga ayyukan gwamnati a cikin shekaru hudu da suka gabata.
Bego ya ci gaba da bayyana cewa Buni ya bayyana manyan nasarorin da wa’adinsa na farko ya samu sakamakon kwazon aiki, sadaukarwa da kuma hakuri da ‘yan majalisar zartarwar jihar suka yi rika nunawa a tsawon wannan lokaci da ya ambata.
Tun da farko da yake yiwa manema labarai  karin bayani kan wasu ayyuka da aka amince da su a karkashin ma’aikatar sa a yayin zaman majalisar, kwamishinan ma’aikatar ayyuka na jiha injiniya.  Umar Wakili Duddaye, ya ce majalisar ta amince da sama da naira biliyan talatin, (₦30 Billion) domin gudanar da ayyuka daban-daban a fadin jihar.
A cewar Kwamishinan, an raba ayyukan zuwa kashi uku wadanda suka hada da;  hanyoyin garin Nguru, Gashua, Potiskum da Geidam.
“Kashi na biyu sabbin ayyuka ne da aka fara, wadanda suka hada da gina titin kilomita 18 daga Fika zuwa Maluri, 25.5km daga Gashua zuwa Dumburi- Masaba, kilomita 4.5 akan hanyar Nguru zuwa Karasuwa Galu, da kuma kilomita 18 daga Bukarti zuwa Toshia cikin karamar hukumar Yunusari duka a Jihar ta Yobe.
“Yayin da kashi na uku na aikin shine sake gina wasu hanyoyi da suka lalace a lokacin daminar bara 2022 a fasin jihar.”
“Wannan ya hada da sake gina hanyoyin daga Geidam zuwa Bukarti, Baimari zuwa Yunusari da Yunusari zuwa Kafiya har zuwa Kanamma.
Injiniya Duddaye ya ci gaba da cewa, dukkanin ayyukan sun hada da titunan kilomita 93 da za a yi gini, da magudanar ruwa mai nisan kilomita 20 na titunan garin, da kuma kilomita 66 na sabbin hanyoyin da aka kashe kudi miliyan 30,440,740,658,60.
Ita ma cikin jawabinta kwamishinar ma’aikatar kula da aikin gona a jihar Hajiya Mairo Amshi godiyar ta ta nuna bisa ga yadda gwamnan ya ba su damar bada gudummawarsu wajen kara habaka jihar musamman ta fuskar aikin gona inda gwamnatin Jihar a kowace shekara bata yin kasa a gwiwa wajen samarwa manoman Jihar Takin Zamani a wadace cikin farashi mai rahusa tare kuma samar da kayayyakin aikin noma da suka hada da motocin Tarakta da sauran Kayayyakin taimakawa amfanin gona don ya habaka.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.