Daga Imrana Abdullahi
An bayyana taron da yayan jam’iyyar APC suka yi a garin Abuja a matsayin taron son ci gabansu kawai ba tare da la’akari da jama’a ba.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani dan asalin Jihar Zamfara mai kishin al’umma Alhaji Bashir Nafaru da ke fafutukar kwato yancin jama’a a Jihar Zamfara da kasa baki daya.
Alhaji Bashir Nafaru ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu.
Bashir Nafaru ya ci gaba da tofa albarkacin bakinsa da cewa wadanda suka yi taro a garin Abuja hakika su da suke yan asalin Jihar Zamfara sun yi ne kawai domin biyan bukatun kashin kansa.
“Mu a matsayin mu na yan Jihar Zamfara masu kishin Talakawa wannan taron da suka yi ba ta yadda za a yi su goyi bayan wannan taron da wasu yan siyasa suka gudanar a Abuja, mu Akidar mu ita ce ba wai mutum ko jam’iyya kawai muke yi ba fatan mu shi ne kawai mu yi mutumin da zai taimakawa yan asalin Jihar Zamfara da zai kawo masu tattalin arziki ya kawo mafita a kan harkar tsaron lafiya da dukiyar jama’ar Jihar kuma ya tabbatar ya ba su ingantaccen ilimi a sako da gungun Jihar baki daya, don haka taro ne da ya shafi kansu kawai domin sasantawarsu kawai a tsakaninsu kuma mu a Jihar Zamfara ba shi ne damuwarmu ba damuwarmu shi ne a samu zaman lafiya tare da karuwar arziki a koda yaushe kawai”.
Fatan mu shi ne Allah ya sa a tafiyar da za a yi a nan gaba Allah yasa a samu zaman lafiya da ciyar da jiha da kasa baki daya gaba.