Home / Labarai / Muna Goyon Bayan Maganar Ministan Tsaro Bello Muhammad Matawalle- Dokta Suleiman Shu’aibu

Muna Goyon Bayan Maganar Ministan Tsaro Bello Muhammad Matawalle- Dokta Suleiman Shu’aibu

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, dan kungiyar kare hakkin bil’adama ne da wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afirka baki daya ya bayyana cikakken hadin kansa da goyon baya ga ministan tsaro Dokta Bello Muhammad Matawalle a game da batun yankin arewacin Najeriya da wasu masu cewa su ne Dattawa suka yi.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a wani babban taron manema labarai na kasa da kasa

A matsayin mu na matasan Afirka masu kula da abubuwan da ke zuwa su dawo muna tare da Ministan tsaro Dokta Bello Muhammad Matawalle, a bisa maganar da ya yi a kokarinsa na kare mutinci da martabar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ci gaba da yin kira ga daukacin iyaye Dattawan Arewa cewa shin tun da ake kashe kashe a yankin arewacin Najeriya sun ta ba kiran wani babban taro a game da hakan domin tattauna batutuwan da ke addabar arewacin Najeriya? Ko kuma su iske shugaban kasa ko su kira dukkan ministocin nan na Arewa domin suzo su zauna su fada masu abin da ya dace duk da suna da wannan dama amma ba su yi ba.

” ko a lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ke mulki ai ya dauki ministoci da dama musamman ma manya kai har da kanana duk ya hannantawa arewa, amma me suka yi?

“Saboda haka idan mai girma minista ya tashi tsaye a kan kare mutuncin shugaban kasa ai ya yi dai- dai, don haka muna bayansa muna kuma tare da shi a koda yaushe, saboda shi shugaban kasa fa wata hukuma ce a kasa don haka dole ne a kare ta a koda yaushe don haka dole a kare martabar hukuma, don haka mun Gamsu da aikin da Bola Ahmed Tinibu yake yi kuma muna yin kira a gare shi ya ci gaba da yin ayyukan nan na kwarai”.

Dokta Shinkafi, ya kara jaddada cewa ya dace kowa ya Sani cewa duk abin da ya tabarbare ya samu tabarbarewar ne tun lokacin Buhari, domin Bola Tinubu yazo ne ya na ta aikin gyara a fannoni da yawa kuma ya dace a rage ma shugaban kasa, ta yaya za a gyara Najeriya a cikin watanni Takwas, ya dace a Sani cewa abin da Buhari ya lalata, shi ne Bola Tinubu ke gyarawa a yanzu, kuma a yanzu ba lokacin siyasa ba ne balantana iyayen mu da kakannin mu su rika yin batutuwan siyasa. A halin yanzu ana yin ayyukan raya kasa ne da har aka ceto kasar a fannoni daban daban  .

“Kufa duba a kullum sai an kashe mutane a kowane bangaren Najeriya musamman ma a arewacin Najeriya, amma ta yaya su wadannan Dattawan na Arewa shin ta yaya ba su tashi takanas suje wajen shugaban kasa su gaya masa baki da baki cewa ya dace a Dakatar da wannan lamarin, su fito da dukiyarsu da dukkan kwarewarsu su taimakawa Gwamnati domin a tsayar da batun, amma har yau ba a yi hakan ba sai maganganun shaci fadi na shan shayi kawai. Shi kuwa ministan tsaro ya tashi ya na kare shugaban kasa da kare jama’ar Arewa ai duk dai- dai yake abin da ya yi.

Shi ne ke kokarin tashi tsaye ya kare mutuncinsa da na Gwamnati da shugaban kasa  kuma ya na yin hakan ne da duk dukiyarsa.

“Mu a iya sanin mu mai girm Bello Muhammad Matawalle na ganin mutunci Arewa da Dattawan arewan baki daya kuma ba ta yadda wani mutumin Dattawan Arewa zai tashi ya je wurin ministan tsaro har ofishinsa ya gayawa ministan ga abin da za a yi, ya kiya ko ba zai dauka ba ko kin amincewa. Kuma ina wasu shugabannin  Arewa za su ce sun je wurin shugaban kasa Tinubu, domin su gaya masa abin da ya dace a Arewa ko yake faruwa a Arewa amma yaki yarda su gan shi, don haka ba maganar a koma gefe ana ta cece- kuce ba, muna magana ne na yadda za a ceto Arewa da halin da ake ciki. Saboda haka muna gaya wa jama’a wanda zai ci zabe a shekarar 2027, Bola Ahmed Tinubu ya ci zabe da gagarumin rinjaye ya zama shugaban Najeriya don haka muke goya masa baya a ceto kasar nan ba wai wannan ya yi nan ba wancan ya yi can ba ayi ta fandare fandare ba gaira ba dalili ba.

Domin haka muke kara fadakar da jama’a cewa ya dace dole ne a tashi tsaye goyawa shugaban kasa baya ta yadda za a samu ci gaba.

” Muna kara tabbatarwa da duniya cewa a matsayin mu na matasan arewacin Najeriya mina goyon bayan ministan tsaro Dokta bello Mihammad Matawalle kuma kungiyoyin Kudancin Najeriya duk sun goya mana baya a kan maganganun da ministan tsaro ya yi na cewa baikamata ba su fito da maganar siyasa domin a yanzu ya dace ne kawai a dauki sahun ya za a yi komai ya dauki saiti, yaushe wadannan Dattawan suka ta fi wajen wata ma’aikata ko ta Aikin Gona su gaya masa ga abin da ke faruwa daga nan a dunguma a ta fi wurin shugaban kasa su shaida masa cewa ga abin da za a yi amma shugaban kasa bai yi ba, to, idan bai yi ba sai a samu matsala amma dai ba a yi hakan ba.

Dokta Suleiman Shinkafi ya kara da cewa suna yin kira ga Dattawan Arewa cewa ya dace su yi amfani da fasaha, basira da dukkan damarsu su ga yadda za a daina kashe kashen jama’ar nan da sauran matsalolin da ke addabar kasar nan, idan kuwa ba a yi hakan ba to, har yau ana cikin ruwa zundum. Don haka muna yin kira ga wadannan Dattawan da su mayar da wukarsu a cikin kube, saboda ya dace a Sani cewa ministan tsaro ya yi magana ne domin ya gaya wa dattawannan gaskiya kuma ya kare muradun Arewa don haka muna tare da ministan tsaro kuma ba zamu bari wani abu ya kawo mana taimaki cikin wannan tafiyar ba kuma duk abin da ya ce gaskiya ne.

Muna yin kira ga Dattawan arewa da su ba ministan tsaro Dokta Mihamamd Bello Matwalle cikakken hadin kai da goyon baya domin suk kun san abin da ya dace a koda yaushe.

Muna kuma yin kira ga dukkan matasan Arewa da na kasa baki daya da du bayar da goyon baya domin Dimokuradiyya ta samu ci gaban da ya dace.

About andiya

Check Also

Religious Harmony: Faith leaders converge in Kaduna for Interfaith Dialogue 

Media networks have rallied round all faith leaders to join in the inaugural Kaduna Interfaith …

Leave a Reply

Your email address will not be published.