Home / News / ZA MU SAMAR DA KUDIN DA NNPC BA ZA TA SAMAR BA DA HARKAR NOMA – ALIYU WAZIRI

ZA MU SAMAR DA KUDIN DA NNPC BA ZA TA SAMAR BA DA HARKAR NOMA – ALIYU WAZIRI

IMRANA ABDULLAHI

Shugaban kungiyar Noman zamani ta kasa NAMCON Alhaji Aliyu Muhammad Waziri Santurakin Tudun wada Kaduna da ake yi wa lakabi da dan marayan Zaki ya bayyana wa manema labarai cewa za su iya samar wa da Najeriya makudan kudin da kamfanin matatar man fetur na NNPC ba za su iya samarwa ba da harkar Noma.

Alhaji Waziri dan marayan Zaki ya tabbatarwa manema labarai cewa ta yaya wanda ke sayar da litar mai a kasa da naira dari biyu zai iya samar da abin da ake samu sama da naira dubu daya a matsayin man Girki kwatankwacin lita daya?

Saboda haka ya ce bangaren su na Noman zamani a shirye suke su sama wa Najeriya kudin shigar da ba wani bangaren da zai iya samar da shi a Gwamnati.

“Mun shigo da tsarin Noman zamani da ake yin sa a zamanance da na’urorin yin Noma sabanin irin yadda ake yinsa a can baya, inda ake amfani da yin aikin Gona da hannu ko kuma Daurawa Shanu Garma wanda dalilin hakan duk inda za a samu amfanin Gona buhu Goma to, idan an yi amfani da kayan Noman zamani za a iya samun Buhunan da za su kama daga Talatin zuwa Arba’in da wani abu wannan shi ne Noman zamani.

Ya ce ga kuma kayan Noma na zamani kama daga fashin haki da Takin zamani irin na feshi da ke bayar da yabanya mai kyau da inganci.

Ya kara da cewa tun a shekarar ” 2017 da ya fara gudanar da wannan aikin babu wani da ya bashi ko sisin Kwabo da kudinsa kawai yake aiwatar da komai domin kishin gina kasa Najeriya ta bunkasa.

Saboda haka muke kiran jama’a da su hada hannu da kungiyar tabbatar da Noman zamani ta NAMCON domin samun kwalliya ta biya kudin sabulu.

Alh Dokta Aliyu Muhammad Waziri OON Dan’Marayan Zaki, Santurakin Tudun Wada, Dujiman Bwari Abuja kuma Hasken Matasan Arewa, ya ce wannan tsarin Noman zamani a yanzu ya kai ga Jihohin Najeriya sama da Ashirin da biyar da ake saran cikin wannan watan za a yi babban taro a Kano domin kaddamar da fara Gina gudan kiwin Kaji domin samawa jama’a aikin yi da dogaro da kai.

” muna da tsarin da babu irinsa na sayen kayan amfanin Gona a yanar Gizo da kowa ne mutum zai iya sayen amfani daga ko’ina yake a duniya da dai sauran tsare tsare da dama”, inji dan marayan Zaki.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.