Home / News / Dikko Radda Mutumin Kirki Da Al’umma Za Su Dogara Da Shi – Honarabul Kuraye

Dikko Radda Mutumin Kirki Da Al’umma Za Su Dogara Da Shi – Honarabul Kuraye

IMRANA ABDULLAHI A KADUNA

An bayyana dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin tutar jam’iyyar APC Dokta Dikko Umar Radda, a matsayin mutumin kirki, mai gaskiya da rikon Amana da al’umma za su dogara da shi domin ci gaban Jiha tare da al’ummarta baki daya.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mutumin da ya dade ya na huldar arziki da Dikko Umar Radda, tun daga lamarin siyasa da kuma sauran harkokin rayuwa Honarabul Lawal Isa Kuraye a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kgarin Kaduna.

Saboda irin wannan Nagarta da dan takarar Gwamnan yake da shi ne yasa aka yi kira ga daukacin al’umma da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Dokta Dikko Umar Radda, dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin tutar jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Dan majalisar dokokin Jihar Katsina Honarabul Lawal Isa Kuraye mai wakiltar karamar hukumar Charanchi a lokacin wata ganawa da manema labarai a Kaduna.

Honarabul Kuraye ya ci gaba da bayanin cewa hakika dan takarar Gwamnan Jihar Katsina mutum ne mai kyawawan halaye mai natsuwa ga son ci gaban jama’a, kuma wani abin sha’awa ya na da kokarin rikon gaskiya da Amana, mai kokarin yin shawara da a kan duk wani lamarin da za a yi domin jama’a, kuma a koda yaushe ya na karbar shawarar da shugabanninsa sula bayar domin a samu dai – daituwar al’amura baki daya.

Kamar yadda ya bayyana, Dokta Dikko Radda ya na da nagartar juriya wajen daukar matakai masu gauni kuma ya kan yi sassauci domin inganta rayuwar al’umma.

Sai ya ce mutanen da suke da nagartattun halaye irin wannan ba su da yawa a cikin al’umma a yau, saboda haka al’ummar Jihar Katsina masu zabe ya dace su yi wa Allah godiya bisa irin sa’ar da sula yi na samun Dokta Dikko Umar Radda a matsayin shugaba.

Irin halin da ake ciki a Jihar Katsina hakika ya na bukatar mutum mai kokari da zimmar aiki hade da juriya da ke yin aiki tukuru da zai yi aikin maganin kalubalen tsaro da tattalin arziki.

Dikko kwararren dan siyasa ne da ke yin aiki a matsayinsa na masanin makamar mulki, misali ya taba zama shugaban karamar hukuma,mataimaki ga dan majalisar tarayya kuma Mamban jam’iyyar APC a matakin kasa. Kuma ya yi aikin shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Katsina, wanda daga nan aka nada shi a matsayin Darakta Janar, na hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu (SMEDAN) wanda shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi.

Lokacin da ya kwashe a matsayin Darakta Janar a hukumar SMEDAN ya yi aiki tukuru wajen ciyar da hukumar gaba a matakin kasa da kuma matakin kasa da kasa wanda hakan ya haifar da samun ci gaban tattalin arzikin kasa.

Domin tabbatar da irin kwarjininsa a siyasa Dokta Dikko Umar Radda Radda samu nasarar lashe zaben fitar da dan takarar Gwamnan Jihar katsina, inda ya kayar da  yan takara guda Takwas ya zama dan takarar Gwamna a zaben 2023 karkashin jam’iyyar  APC.

Bayan kammala zaben fitar da dan takara, dukkan sauran yan takarar guda Bakwai sai suka yi mubaya’a kuma suka amince da yin aiki tare domin ci gaban jam’iyya.

Lokacin da aka kaddamar da Yakin neman zaben Gwamnaa kusa da watan Disamba a garin Faskari na karamar hukumar Faskari a Jihar Katsina, ,hakika irin yadda jama’a suka taru alamace da ke nunin cewa masu zabe sun Gamsu kuma sun yi mubaya’a.

Da yake jawabi game da kasancewarsa dan majalisa mai tsayawa takara karo na uku Honarabul Kuraye, ya ce niyyarsa ita ce ya koma majalisar Jiha domin ya ci gaba da bayar da gudunmawarsa wajen samar da ingantattun dokoki da za su inganta rayuwar al’ummar Jihar katsina.

A game da kokarin da yake yi domin samar da ci gaban mazabarsa? Sai ya ce ya samar da wani tsarin da ake kira LK wanda sakamakon hakan ya samar da malaman makaranta guda 13 a cikin shekaru biyu. Sakamakon hakan a irin nasarar da aka samu karkashin shirin “LK – Power” sai Gwamnatin Jihar Katsina ta yi alkawarin daukarsu aikin S – Power na Gwamnatin Jiha.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.