Home / KUNGIYOYI / DOLE NE ALKALAI SU YI AIKI DA GASKIYA DA TSARON ALLAH – ALKALI NASIR

DOLE NE ALKALAI SU YI AIKI DA GASKIYA DA TSARON ALLAH – ALKALI NASIR

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Alkalin kotun shari’ar Musulunci da ke Mando, Alkali Muhammad Nasir da aka yi wa lakabi da Alkalin fita kunya ya bayyana cewa babban dalilin da yasa aka karramashi ya biyo bayan irin kokari, kwazon aiki tare da jajircewa ne da yake yi a kullum wajen aiwatar da aikin shari’a a kotun da yake aiki.
Kungiyar Kwaryar Tudun wada Kaduna tare da hadin Gwiwar Amale 24 ne suka Karrama Alkalin saboda irin adalcin da yake yi wajen aiwatar da aikin shari’a a kotun shari’ar Musulunci da ke Mando Kaduna.
“Wannan karramawar da aka yi Mani zai kara taimaka Mani kwarai in jajirce domin aiki ne na Amana da aka ba ni domin jama’a, ya kara mani kaimi kwarai kuma na godewa iyaye na, shugabanni na da wadanda suka shirya Mani wannan gangamin domin bayyana abin da nake da kuma wallafa mujalla musamman”,.
Alkali Nasir ya ce ” ya zama dole a kan kowane Alkali tun daga alkali na farko wato Cif Joji har zuwa ga Alkali na karshe ya zama wajibi ga kowane Alkali ya bayar da gudunmawar da zai iya bayarwa na yin kokari wajen amsarwa mama’s Hakkinsu da kuma yin abin da duk yakamata”.
Ya kara da cewa su a matsayinsu na Alkalai ana samun wasu matsaloli a kan matasa, na farko shi ne son zuciya, yan dauke dauke da yan shaye shaye, muna samun matsaloli da yawa a kan hakan don haka kaga koda yaushe aka kawo su wurin mu sai mu duba abin da yakamata muyi na sassauci da kuma bin doka da oda”, inji Alkali Nasir.
“Kamar yadda na gaya maku wannan aiki ne na Amana don haka dole ne mutum ya tabbatar ya yi abin da duk ya dace ya yi tare da bin doka da odar aiki, domin aikin Ibada ne duk abin da ka yi Allah na kallonka don haka wajibi ne a kan kowane Alkali ya yi abin da ya dace, idan ma bai yi ba to, Amana ne Allah zai tambayeka wata rana”, Inji Alkali Muhammad Nasir, na kotun Mando Kaduna.

About andiya

Check Also

The Daily Hug For Appreciation 2023

The daily hug for 28/11/23 is this appreciation of an echo shared by my dear …

Leave a Reply

Your email address will not be published.