Home / Labarai / Dubban Al’ummar Garin Gusau Sun Yi Murnar Dawo Da Layukan Sadarwa 

Dubban Al’ummar Garin Gusau Sun Yi Murnar Dawo Da Layukan Sadarwa 

Mustapha Imrana Abdullahi
Dubban al’umma a garin Gusau fadar Gwamnatin Jihar Zamfara sun bayyana gamsuwa da irin yadda aka dawo da layukan wayar sadarwa a cikin birnin Gusau, bayan shade kwanaki a kalla Talatin (30) babu layukan baki daya.
Jama’ar dai sun yaba wa Gwamna Matawalle bisa wannan Namijin kokarin da ya yi.
Gwamnatin Jihar Zamfara tare da hadin Gwiwar hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasa (NCC) suka hada Gwiwa inda aka rufe layukan sadarwar domin taimakawa jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu wajen yaki da yan bindiga masu satar Shanu da mutane.
 Kamar yadda Gwamnan na Zamfara ya ce rufe layukan sadarwar an yi shi ne tare da sanin dukkan masu ruwa da tsaki a Jihar domin a yaki yan bindigar da suka addabi Jihar baki daya.
 Wadansu matasan da muka tattauna da su a unguwar Tudun wada, Gada- biyu, Bakin kasuwa, tsohuwar tashar mota, Hayin Mai Gemu da unguwar Dallatu duk sun bayyana jin dadinsu da umarnin da Gwamnan ya bayar domin a dawo da layukan wayar sadarwar ta yadda jama’a za su ci gaba da gudanar da harkokinsu.
Umar Sulemain Anka wani mai shago be a unguwar Tudun wada ya bayyana faruwar wannan lamarin da cewa wata gagarumar sadaukarwa ce domin a samu nasarar yaki da yan Ta’adda a Jhar Zamfara,sakamakon hakan ne ya bayyana Gwamna Matawalle a matsayin wani shugaba mai kokarin garin ya ceto Jihar daga hannun yan Ta’adda domin yadda masu karamin karfi za su samu cimma nasara a cikin rayuwarsu ta yau da kullum.
Hajiya Amina Musa Mai Shadda kuwa cewa hakika al’amarin yan Ta’adda ya zamo wani babban kalubale da ke bukatar a magance shi ta hanyar sadaukarwa, sai ta bayyana farin cikinta da irin matakin da Gwamna Bello Matawalle ya dauka na dawo wa da layukan sadarwa a yanzu.
Sanarwa da Dawowa da layukan sadarwar an bayyana shi ne a ranar Juma’a inda kwamishinan kula da harkokin sadarwar Jihar Zamfara Malam Ibrahim Dosara ya sanar.
Bayan dawowa da layukan wayar, an kuma sassauta a babban birnin Jihar na Gusau inda a yanzu za a ci gaba da gudanar da al’amuran saye da Sayarwa kamar yadda saba.
Dosara ya kuma ce dawowa da layukan sadarwar an takaita shi ne kawai a cikin garin Gusau, sauran kananan hukumomi kuma za a duba na su nan ba da jimawa ba, idan harkokin tsaro sun inganta.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.