Home / Lafiya / Duk Wadanda Aka Gwada A Nijeriya Ba Su Dauke Da Cutar Korona – NCDC

Duk Wadanda Aka Gwada A Nijeriya Ba Su Dauke Da Cutar Korona – NCDC

Mustapha Imrana Abdullahi

CIBIYAR kula da cututtuka ta kasa (NCDC) a ranar Alhamis ta bayyana cewa dukkan wadanda suka kammala yi wa Gwajin cutar Korona babu wanda ke dauke da cutar.

Cibiyar ta tabbatar da cewa dukkan mutane 31 da ake zargin sun kamu da cutar Korona birus babu wani da ke dauke da cutar. “Wannan na nufin cewa kenan Nijeriya ba wanda ke dauke da wannan cuta kuma kasar babu cutar Korona birus baki daya”.

Daraktan kulawa da ayyukan gaggawa na kota kwana Dakta John Oladejo ya bayyana hakan a wajen wani taro ne a Sakkwato domin duba wa tare da tattauna samun yanayi irin na ko ta kwana inda aka tattauna a kan cutar Lassa da Korona Birus . Taron dai jami’ar Dan fodiyo Sakkwato ce ta shirya shi.

Ya bayyana cewa cibiyarsa na da dukkan na’urorin da za su iya tabbatar da wannan cutar, ya kara da cewa ana duba dukkan masu shigowa kasar nan domin tabbatar da ba a samu wani ya shiga da wani abu da ba a aminta da shigarsa kasar ba.

Ya ci gaba da cewa da akwai dakunan Gwaje gwaje guda uku da suka hada da dakin Gwaje gwaje na Abuja, wurin Gwaje gwaje na asibitin koyarwa na jami’ar Legas da kuma wurin gwaji na Irrua da ke Jihar Edo.

Ya ce ranar 23 ga watan Fabrairu, kasashe 29 ne cutar ta shafa da suka hada da China, Thailand, Japan, Jamhuriyyar Korea, Amurka, Jamhuriyyar Singapore, Vietnam, Australia, da tarayyar kasar Dimokuradiyya ta Nepal.

Sauran da suka kamu sun hadar da Faransa, Malaysia, Canada,Kambodiya, Sri Lanka, Jamus, Tarayyar Larabawa, Philippines, India, Finland, Italiya, Rasha, Spain, Sweden, Ingila,Belgium, Egypt,Iran, Lebanon, da Israila.

Ya ci gaba da cewa a dai ranar 23, alkalumma sun tabbatar da cewa dakunan Gwaje gwajen da suka tabbatar da kamuwa da cutar sun kai 78,811 daga cikinsu akwai 77,042 daga kasar China da ya bayar da tabbacin kashi 97.8) Sai kuma yawan wadanda suka mutu ya kai dubu 2,462 wadanda daga cikinsu 17 daga wajen kasar China ne .

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.