Related Articles
Daga Imrana Abdullahi, Kaduna
…Gamayyar ’Yan Takarar Majalisar Dokokin jihar Kaduna a zaɓen da za a sake na Mazaɓar Maƙera da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu a jihar Kaduna sun fito sun nuna mara wa Honarabul Yusuf Dahiru Liman baya, a matsayin mutumin da za su zaɓa don wannan matsayi.
A wani taron manema labarai da suka kira jiya a Kaduna, wanda ɗaya daga cikin su, Honarabul Nura Mohammed Sarki ya jagoranta, ya yi bayanin cewa sun sun ɗauki wannan mataki ne bisa la’akari da cancantar Hon. Liman, wanda suka ce da ma dai shi ne a kan wannan kujera, kuma sun ga kamun ludayin sa akwai haske a lamarin.
Nura Mohammed ya ce haɗin kan ‘yan takarar jam’iyyun siyasa a mazabar Maƙera duk sun amince da Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman a matsayin ɗan takara ɗaya tilo a zaɓen wasu mazaɓu guda biyar na Maƙera na majalisar dokokin jihar Kaduna.
“Mu ’yan takara daga sauran jam’iyyun siyasa a jihar Kaduna mun taru mun amince da Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman a matsayin ɗan takarar ɗaya tilo a zaɓen da za a yi a rumfuna biyar na Maƙera a Kaduna ta Kudu domin samun wakilci nagari, kuma muna yin hakan ne gabanin sake gudanar da zaɓen da aka tsara a ranar 3 ga Fabrairu, 2024.
Ya ƙara da cewa, “Taron na haɗin guiwar ya ƙara jaddada imaninsu na cewa Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman yana da kyawawan halaye na wakilcin al’ummar mazaɓar jihar Maƙera bisa gaskiya, tare da ƙudurin ci gaban mazaɓar mu da ma jihar Kaduna baki ɗaya”.
“Haka nan muna kira ga ɗaukacin mambobin mu da mazauna mazaɓun nan biyar da abin ya shafa a mazaɓar jihar Maƙera da su fito gangamin goyon bayan Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, tare da kaɗa ƙuri’un su domin nuna goyon bayan su ga takarar sa a kodayaushe yana nuna zurfin fahimtar al’amuran da ke addabar mazaɓar mu domin yana da kyakkyawar manufa ta makoma mai kyau.
Hon. Nura Mohammed Sarki ya kuma bayyana cewa dukkanin jam’iyyun siyasar da suka shiga, sun kuma tabbatar da aniyar su ta ganin an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci ba tare da tada hayaniya ba.
Don haka suka yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, wanda za a yi a ranar 3 ga Fabrairu, 2024.