Home / Labarai / Gobara: Honarabul Abdulkarim Kero, Ya Jajanta Wa Masu Shaguna, Sarki Tare Da Jama’ar Unguwar Sanusi

Gobara: Honarabul Abdulkarim Kero, Ya Jajanta Wa Masu Shaguna, Sarki Tare Da Jama’ar Unguwar Sanusi

Daga Imrana Abdullahi

Dan Majalisa Mai Wakiltan Kaduna Ta Kudu a Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke Abuja, Honarabul Abdulkarim Hussaini Ahmad da ake yi wa lakabi da  (Mai Kero) ya jajanta wa Masu shaguna da ibtila’in gobara ya afkawa a layin Muhammadu Wule kusa da ‘Yar Kasuwa da ke Unguwar Sanusi a jiya Asabar.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sharifudeen Ibrahim Muhammad.    (Dan Jarida) mai taimakawa dan majalisa Kero a kan harkar kafofin yada labarai da sadarwa, da aka rabawa manema labarai a Kaduna.

Dan majalisa Abdulkarim Mai Kero ya fitar da sakon jajen ne ta hannun me magana da yawun sa, Sharifudeen Ibrahim Muhammad (Dan Jarida) Jim kadan bayan afkuwan lamarin da ya lakume shaguna hade da ‘Dakuna da yawan su ya Kai shida.

Dan majalisa Mai Kero ya nuna alhinin sa bisa lamarin da ya ja hasarar dukiya da dama, Wanda ba kiyesta yawan miliyoyin ba.

Wadan da lamarin ya shafa sun hada Malam Suleiman Me lemu wanda ya rasa shago hade da dakin kwanan sa, Mal Mahmuda Me Shagon Manja, sai Malam Murtala Me Shagon Provision, sauran sun hada Tano me kayan Hatsi tare Maman Maryam me kayan Dinki.

Daga bisani, Hon. Kero ya yi addu’ar Allah Ya mayar da arziki, Ya sa dukiyar da aka rasa ta zamo kaffara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.