Home / News / Gwamna AbdulRahaman AbdulRazak Zai Jagoranci Kwamitin Mutane Takwas Domin Duba Batun shiyya a APC

Gwamna AbdulRahaman AbdulRazak Zai Jagoranci Kwamitin Mutane Takwas Domin Duba Batun shiyya a APC

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Shugaban kwamitin rikon jam’iyyar APC na kasa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron APC na kasa wanda ya kasance kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da nadin kwamitin da zai yi aiki a kan batun shiyya shiyya gabanin babban zaben jam’iyyar.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Sanata Dokta, John Jemes Akpanudosehe sakataren babban kwamitin shirye shiryen babban zaben na kasa
Ga dai sunayen mutanen kamar haka:
1.Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahaman AbdulRazak a matsayin shugaba.
2. Mataimakin shugaban majalisar Dattawa ta kasa Ovie Omo Agege a matsayin mataimakin shugaban kwamitin.
3.Farfesa Etim Nyang a matsayin Mamba.
4. Dokta MB Shehu a matsayin mamba.
 5. Kwamared Mustapha Salihu a matsayin mamba
6. Sanata Teslim Folarin a matsayin Mamba
7. Alhaji Sadeeq Sule-Iko Sami  a matsayin Mamba
8. Mataimakin Gwamnan Jihar Anambara Nkem Okeke a matsayin Sakatare.
Ana kuma saran kwamitin ya mika rahotansa a ranar Litinin 7 ga watan Maris, 2022.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.