Home / News / Gwamna Uba Sani Na Ta Ya Yan Najeriya Murnar Nasarar Wasan Da Aka Yi – Sa’idu Dibis

Gwamna Uba Sani Na Ta Ya Yan Najeriya Murnar Nasarar Wasan Da Aka Yi – Sa’idu Dibis

Daga Imrana Abdullahi

Mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar  Uba Sani a kan harkokin wasanni Sa’idu Dibis ya bayyana matukar murna da farin cikin da Gwamna Uba Sani ke taya daukacin yan Najeriya game da nasarar da aka samu a kan kasar Angola a wasan da aka yi tsakanin kasashen biyu.

“Kamar yadda na fada wa wadansu tun farko a lokacin gasar cin kofin kasashen Afirka na Goma sha tara,mun samu nasarar shiga irin wannan gasar sau Goma sha tara kenan. Amma ni a gare ni ina ganin wannan kulab din kamar irin wancan kulab din da suka yi wa Najeriya wasa ne a shekarar 1994 domin na ga mai horas da yan wasan na yin amfani da basira da kwarewa sosai, wasu masu kallon kwallon za su ga kamar irin a rika taba kwallo shi ne kwallo amma duk mai basira da fakira a kan kwallon zaka gane cewa mai horas da yan wasan na amfani ne da abin da ake cema basirar horas wa mai cike da dabaru.

Dibis ya ci gaba da bayanin cewa daman can sai da ya gaya wa jama’a cewa zamu rika cin wasannin da Najeriya za ta rika bugawa amma ba da kwallaye masu yawa ba, domin kamar yadda ya ce mai horas da yan wasan na yin amfani ne da wata basira da tsohon mai horas da yan wasan kwallo na kulab din Chelse Morinho ya rika yin amfani da ita kuma shi ya fara kawo ta a rukunin wasan kasar Ingila, a wannan irin yanayi ne har ya ci gasar da ake bugawa har sau biyu a Jere. Saboda haka ne nake tabbatarwa da suk wani wanda ya san kwallo da mai son wasan kwallon ma baki daya cewa duk mai yin amfani da irin wannan tsarin da Morinho ke amfani da shi lallai za a samu nasara sai dai ace ana yi wa Allah godiya a koda yaushe.

” Duk da yana cikin yanayin tattalin arziki a Najeriya to, ya dace jama’a su Sani ba wai a Najeriya bane duk magana ce da duk duniya radadin tattalin arziki na damun jama’a, amma samun wannan nasarar cikin yardar Allah yasa mutane sun dan ji dadi kuma idan Allah ya yarda za a samu nasarar cin kofin sai dai ina rokon yan Najeriya da a Sanya yan wasannan a cikin addu’a muga mun samu nasara a kan kasar Kebbad ko kasar Afirka ta Kudu da za a yi wasan kusa da na karshe a ranar Laraba mai zuwa in Allah ya amince”.

Hakazalika, Mataimakin na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna a kan harkokin wasanni ya mika wa jama’a albishir daga mai girma Gwamnan Jihar Kaduna cewa “tun zuwan mu ni da kwamishinan wasanni da mai girma Gwamna ya nada an yi tsarin ganin an canza Fasalin harkar wasanni baki daya a Jihar Kaduna kuma ba wai mu ne muka yi wannan tsarin sanyawar ba mai girma Gwamna Sanata Uba Sani ne ya yi kokarin hakan ta hanyar ba mu dama da nuna mana ga abin da yake bukata nan da shekaru hudu masu zuwa ga yadda yake son ya ga Jihar Kaduna ta koma a kan harkar wasanni, in ba ta zo na daya a Najeriya ba to, za ta zama na biyu wajen gogayya da duk wanda ke tunanin hakan ne ma jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani aka karbi filin wasanni na tunawa da Ahmadu Bello da ke na Kaduna a yanzu katafaren filin ya dawo hannun mallakar Jihar Kaduna domin yarjejeniyar da aka yi da Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar wasanni ta tarayya kuma da yardar Allah ana karbar wannan fili na Ahmadu Bello sai Gwamna ya zuba makudan kudi masu yawa domin yin gyaran filin aka zuba naira biliyan biyu da nufin a canza wa filin wasan kamanni baki daya kuma bayan wannan ina son gaya wa masu karatu da son harkar wasanni cewa mai girma Gwamna da kansa ya sa za a mayar da filin wasa na cikin garin Kaduna katafaren filayen wasanni kala daban daban domin in an ce arena zaka ga akwai wurin yin sinima,wurin dambe irin na Batire kuma akwai wurin yin bukunkuna da kuma wurare daban daban wanda da yardar Allah har ya rigaya ya yi shiri kuma duk sun dauki saiti da yardar Allah kwanan nan mutanen Jihar Kaduna za su ga wani abu sabo da zai kara karfin tattalin arzikin Jihar Kaduna kuma ya kawo wa jama’a hadin kai da yawa da yardar Allah.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.