Home / News / Gwamna Zulum Ya Hana Bangar Siyasa A Gwoza

Gwamna Zulum Ya Hana Bangar Siyasa A Gwoza

Gwamna Zulum Ya Hana Bangar Siyasa A Gwoza
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana rashin jin dadinsa da irin yadda matasa ke yin bangar siyasa a Goza inda nan take ya soke duk wani nau’in bangar a wurin baki daya.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa ya soke duk wani al’amarin bangar siyasa a karamar hukumar Goza baki daya.
Gwamnan ya bayyana hanin ne a ranar Juma’a lokacin da ya kai ziyara a fadar Sarkin Goza da ya halarci karamar hukumar domin ziyarar aiki.
Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa da irin yadda matasa suka rika gudanar da lamarinsu a lokacin ziyarar. Ya kuma gargadi yan siyasa da ke kokarin kyankyashe yan bangar siyasa da su hanzarta kaucewa irin wannan halayya.
“A matsayin mu na Gwamnati muna yin shirye shirye iri iri daban daban domin kara karfafa Gwiwar matasanmu ta yadda za su zama abin alfahari a cikin al’umma.Hakika a yau ban ji dadin abin da na gani ba,naga matasa dauke da hotunan yan siyasa suna ta hargowa suna kokarin haifarwa da jama’a matsala”.
“Ni bana son irin wannan halayyar, don haka mu yi kokarin hana matasa shiga cikin irin wannan matsala ta bangar siyasa”.
“Ku yan siyasa kuke Jefa matasa cikin iri  wannan halin, bari in gaya maku gaskiya, wannan ba zai iya nuna cewa ku kuna da farin jini ko wani kwarjini ba. Kuma hakan ba zai taba Sanya ni murna ko farin ciki ba, ba kuma za a iya burge ni da irin wannan ba, don haka ba na son hakan irin wannan halayyar ba na son ta ko kadan”.
“Ba za mu goyi bayan duk wani da ke son lalata goben matasan mu ba da kuma makomar Jihar mu. Kuma ba za mu goyi bayanku lokacin zabe ba,ina son ku tabbatar da wannan a cikin zuciyarku”.
“Na hana yin bangar siyasa a Maiduguri kamar yadda lamarin ya faru a garin Biu, don haka Gwoza ba za ta zama wani abu da ban ba. Bari in gargadi dukkanku  daga gobe na bayar da umarni ga jami’an tsaro da su kama duk wani da ke bayyana kansa da cewa shi dan bangar siyasa ne”, inji Zulum

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.