Home / News / Gwamnatin Katsina Za Ta Kafa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida

Gwamnatin Katsina Za Ta Kafa Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnatin iharJ Katsina ta bayyana cewa tana shirin samar da ma’aikatar kula da harkokin  tsaron cikin gida da za ta mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

Gwamna Dikko Umar Radda ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar  NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a fadar gwamnatin jihar.

Wadanda suka sauya shekar sun hada da daukacin shugabannin jam’iyyar adawa ta  NNPP, da magoya bayansu daga shiyyoyin Sanatoci uku na jihar, karkashin Sanata Abdu Yandoma ne ya jagorance su zuwa gidan gwamnatin jihar.

Gwamna Dikko Umar Radda ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar  NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki a fadar gwamnatin jihar.

Wadanda suka sauya shekar sun hada da daukacin shugabannin jam’iyyar adawa ta  NNPP, da magoya bayansu daga shiyyoyin Sanatoci uku na jihar, Sanata Abdu Yandoma ne ya jagorance su zuwa gidan gwamnatin jihar.

Radda wanda ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga al’ummar jihar Katsina da su ba gwamnatinsa cikakken  kai da goyon bayan, ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da mafita mai dorewa kan matsalolin tsaro a jihar.

Gwamnan jihar Katsina ya ce ba ta kowace hanya ake so a ci zarafin kowa ba, sai dai a duba matsalar ‘yan bindiga a Katsina.

Don haka Gwamna Radda, ya shawarci masu ababen hawa da ’yan kasuwar KEKE NAPEP da har yanzu ba su yi rajistar motocinsu da kekuna masu uku ba da su yi hakan cikin makwanni uku.

Gwamna Radda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta nade hannunta tana kallon yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

 Don haka, ya ce ana kuma shirin daukar karin matasa daga kananan hukumomin sahun gaba da ke fuskantar kalubalen tsaro, domin tallafa wa jami’an tsaro a yankunansu a matsayin ’yan banga.  Hakan a cewarsa, yana ganin rashin isassun jami’an tsaro da mazaje da ke aiki a jihar.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.