Home / Big News / Hukumar Kula Da Kiyaye Hadurra Ta Kasa FRSC Ta Jinjinawa Kamfanin Dangote Bisa Daukar Matakan Harkokin Sufurin Kamfanin

Hukumar Kula Da Kiyaye Hadurra Ta Kasa FRSC Ta Jinjinawa Kamfanin Dangote Bisa Daukar Matakan Harkokin Sufurin Kamfanin

 

 

 

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC sun yaba wa kamfanin Siminti na Dangote musamman a bangaren sufurin kamfanin ta yadda suke kula da ka’idojin tuki ta yadda aka samar da gagarumin ci gaban da ya dace sakamakon hakan aka samu gagarumin ci gaban harkar tuki da sufuri, da aka samu raguwar hadurra kwarai a kan titunan Najeriya tun bayan da aka samar da hanyoyin kiyaye hadurra na zamani a kamfanin.

 

 

Hukumar kiyaye hadarin sun bayyana kamfanin Siminti na Dangote a matsayin wani ginshikin harkokin sufuri da suke yin kokari wajen kiyaye dokokin hanya a yayin tuki ba wai a Najeriya kawai ba har ma da yankin Afirka baki daya.

 

 

Da yake gabatar da jawabi a lokacin ziyarar da kamfanin Siminti na Dangote ya kai hedikwatar hukumar kiyaye hadurra ta kasa a ranar Talata, babban jami’in hukumar Shehu Mohammed, yana wa kamfanin ya yi musamman a irin yadda ya samar da sababbin tsare tsaren kiyaye hadurra, sai ya shawarci da su ci gaba da rike wannan tsarin da aka samar kuma ake amfani da shi wanda sakamakon hakan tsarin na kara karfafa harkokin sufuri a Najeriya.

 

 

Kamar yadda alkaluma suka tabbatar tsakanin shekarar 2025 da 2026 sun bayyana cewa kashi 56 aka samu raguwar hadari da ke rutsa manyan motocin sufuri na kamfanin Simintin Dangote, kuma kashi 36 na taguwar munanan hadurra da kuma kashi 52 na raguwar raunuka

 

Kamar yadda babban jami’in hukumar kiyaye hadurra ya bayyana wannan kididdiga ta bayyana a fili cewa irin yadda kamfanin Simintin Dangote ke yin aiki da wannan tsarin kiyaye hadurra a harkokin tuki na cikin gida, abin da aka bayyana da cewa wani al’amari ne abin koyi ga dukkan manyan kamfanonin sufuri masu daukar kaya a duk fadin Afirka.

Ya kara da bayanin cewa samun nasara kamfanin Simintin Dangote na yin amfani da wannan sabon dokokin tuki, cewa idan shugabannin kamfanin suka samu damar yancin kiyaye tsarin dokar tuki, amfanin lamarin zai watsu ne har ga dukkan kasa baki daya.

 

 

 

Tun da farko, shugaban bangaren kula da harkokin Sufuri na kamfanin Simintin Dangote, Murilo Silva, bayani ya yi mai tsawo a kan irin yadda kamfanin ke bunkasa harkokin Sufuri da suka hada da batun ingantacciyar kulawa tare da sanya idanu ta hanyar yin amfani da na’urorin zamani da kuma sabuwar fasahar AI duk da nufin samun kwalliya ta biya kudin sabulu.

 

 

 

Murilo Silva ya kara da bayanin cewa irin yadda aka dade ana yin Ayyukan hadin gwiwa tare da hukumar kiyaye faruwar hadurra ta kasa FRSC wajen samarwa da kuma aiwatar da tsare tsaren inganta harkokin Sufuri a yanzu lamarin na samar da ingantaccen yanayin mai kyau.

 

 

 

Bugu da kari domin ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin tuki a kamfanin ana ƙoƙarin yin amfani da tsarin sai direba na da ingantattun takardun tuki da kuma samun horon da ya dace.

 

 

Babban jami’in kamfanin Dangote mai kula da rukunin kamfanin Dokta James Adenuga, kara karfafa wa ya yi cewa hakika wannan nasarar an same ta ne sakamakon irin yadda shugabancin ya jajirce tare da samun hadin kan shugabannin gudanarwar Kamfanin na samar da sabbin tsare tsare.

Dokta Adenuga ya kara jadda cewa kamfanin Simintin Dangote a tsaye yake wajen kara inganta al’amuran kamfanin da samar da sabbin ƙirƙire ƙirƙire duk da nufin kara ingantawa harkokin kamfanin a koda yaushe ya yadda za su dace da tsarin duniya baki daya, ta yadda za a samu biyan bukata ga kamfanin da kuma al’ummar da kamfanin ke a wurinsu.

 

 

 

Da yake jawabi, jami’in kula da harkokin kula da lafiya, na kamfanin Simintin Dangote Ozovehe Abraham, cewa ya yi kamfanin ya samar da tsare tsaren ci gaba da suke jerawa da zamani domin kula wa da dubawa ta yadda za a iya gane irin yadda halayyar mutum take a koda yaushe.

 

 

 

 

Wannan tsarin zai taimaka wajen bindokar kiyaye hadurra da kuma samun damar gano tsare tsaren tuki zai kuma taimaka wajen ci gaba da bunkasa yanayin tuki mai kyau kamar yadda dokar ta tanadar.

 

 

Mista Ibrahim ya kara da cewa kamfanin Siminti na Dangote a halin yanzu na kara himma wajen ci gaban karfafa ayyukan kiyaye Hadurra duk da nufin samun rage batun hadari a kan hanya kuma an kara daukar matakin samar da Da’a tare da kyakkyawar tarbiyyar gudanar da aiki a kamfanin.

 

 

Ma’aikatan kamfanin Siminti na Dangote da suka kai ziyara hedikwatar hukumar kiyaye Hadurra ta kasa FRSC sun hada da daraktan yanki mai kula da harkokin Sufuri da ke Obajana kanar mai ritaya, Hermant Rana da Charles Theophilus da Dokta Jibrin Abubakar na bangaren kula da harkokin yada labarai da damar da kyakkyawar dangantaka tsakanin al’umma da kamfanin Dangote

About andiya

Check Also

ADC; Ba A Yi Zabe A Shiyya Ta Daya Ba – Sama’ila Makarfi Da Ummu Lu’u Lu’un Matan Zazzau

….Zaben ADC Ya Bayar Baya Da Kura a shiyya ta daya Daga Imrana Abdullahi Ya’yan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.