Home / Big News / ADC; Ba A Yi Zabe A Shiyya Ta Daya Ba – Sama’ila Makarfi Da Ummu Lu’u Lu’un Matan Zazzau

ADC; Ba A Yi Zabe A Shiyya Ta Daya Ba – Sama’ila Makarfi Da Ummu Lu’u Lu’un Matan Zazzau

….Zaben ADC Ya Bayar Baya Da Kura a shiyya ta daya

Daga Imrana Abdullahi
Ya’yan jam’iyyar ADC daga Shiyya ta daya a Jihar Kaduna sun koka bisa matsalar yin rashin zaben fitar da Gwani na yan takarar da za su tsayawa jam’iyyar takara a dukkan matakai tun daga na yan majalisun Jiha,majalisar wakilai na tarayya, majalisar dattawa da dai sauransu.
Ya’yan jam’iyyar ne da suka fito daga shiyyar ta daya da suka hada da mataimakiyar shugabar Mata a Jam’iyyar Zulaihat Abdulkarim da ake kira da Ummu Lu’u Lu’un Matan Zazzau da ta fito daga karamar hukumar Ikara da kuma ɗan takarar majalisar wakilai domin wakiltar al’ummar kananan hukumomin Makarfi da Kudan tsohon Kwamishina a Jihar Kaduna Alhaji Sama’ila Aliyu Makarfi duk sun tabbatar wa da manema labarai a Kaduna cewa duk a iya saninsu zabe bai gudana ba a yankin shiyya ta daya.
Kamar yadda taron manema labarai ya gudana a cibiyar yan jarida ta kasa reshen jihar Kaduna Alhaji Sama’ila Makarfi ya yi magana da manema labarai a cikin harshen Turanci ya yin da ita kuma Zulaihat Lu’u Lu’un Matan Zazzau ta yi wa manema labarai jawabi da harshen Hausa duk sun tabbatar da cewa ba a yi zaben fitar da yan takara ba a yankin shiyya ta daya.
Kamar yadda Sama’ila Makarfi ya bayyana cewa shi a matsayinsa na dan takarar neman kujerar majalisar wakilai kuma wanda ke wakiltar dan takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a karamar hukumar Makarfi da ya dace ya karbi zaben sa na shugaban kasa bai ga an yi wani zabe ba sai dai kawai a kwai wani wurin ma da aka turo yan banga bangar siyasa suka yi ta’adda inda suka kwace kayan zaben suka yi kaca – kaca da kayan don haka ba wani zaben fitar da Gwani da aka yi a shiyya ta daya.
“Mu a matsayin mu na masu rajin kare hakkin jama’a da kuma don a tabbatar da tsarin dimokuraɗiyyar a duk fadin Najeriya ta yaya za a ce jam’iyya kamar ta ADC da ke kokarin ayi tsari mai kyau amma sai ga shi an kasa yin zaben fitar da yan takara a karkashin ta.

A matsayina na shugaba a bangaren mata a wannan jam’iyya ya dace ace ana yin komai na gudanar da zaben nan tare da ni amma sai ga shi kawai sai dai kawai aka rika yin don rai da don zuciya abin da muke gudu tun a can baya kuma muke kokarin kawai da abin da zai cutar da tsarin dimokuraɗiyyar”, inji Lu’u Lu’un matan Zazzau.

Muna yin kira ga daukacin shugabannin jam’iyyar ADC a duk inda suke da lallai su duba wanann lamarin domin ba a yi zaben fitar da Gwani na a shiyya ta daya.
Sun ce an rike kayan aikin gudanar da zaben fitar da yan takara a wannan shiyya ba a yi zaben ba”, kamar yadda suka tabbatar wa da manema labarai a Kaduna.
“A kowace gunduma na ajiye mutanen da za su yi aikin kula da yadda za a yi zaben amma ba mu ga Malaman zaben ba ma ballantana ayi zaben da ya dace ayi”.
“Ko a karamar hukuma ta ta Ikara duk da rashin zuwan  kayan aikin zaben a kan lokacin da ya dace, sai na tambayi Baturen zaben na tambaye shi ina batun kayan aiki ya ce shima bai sani ba”, inji Lu’u Lu’un Matan Zazzau.
Ni a matsayin na na jagora a yankin shiyya ta daya ba a kawo mana wani shaidar batun zabe ba na kayan aikin da za a gudanar da zaben fitar da yan takarar da za su tsayawa jam’iyyar ADC takara ba.
Wadansu kenan daga cikin ya’yan jam’iyyar ADC da suka halarci taron manema labaran
“Na shiga siyasa ne domin in kare hakkin mata da matasa karfi tare da sakawa mata yancin da ya dace da hakkinsu a koda yaushe”.
 Ta kara da cewa, ” da na je wajen wata mazaba domin tun daga Mazaba ta sai da na zagaya zuwa wadansu Mazabu ma amma ban ga komai mai kama da zabe ba sai a wata tashar zabe da na ana yin irin wannan kidayar jama’a da za a fara yin lissafi daga daya a ce biyar Goma ashirin ko Talatin, sai kawai nima na yi masu da wasa na yi kidayar sai can na gaya masu hakika ban amince da wannan lissafin ba a matsayina na shugaba a jam’iyyar ADC a Jihar Kaduna.
A dama Zulaihat Abdulkarim da ake yi wa lakabi da Ummu Lu’u Lu’un matan Zazzau tare da Sama’ila Aliyu Makarfi a lokacin da suke yi wa manema labarai jawabi a cibiyar yan jarida ta Kaduna
Sama’ila Aliyu Makarfi, dan takarar majalisar wakilai ta tarayya domin wakiltar kananan hukumomin Makarfi da Kudan, kuma wanda ke wakiltar dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC a karamar hukumar Makarfi amma ban ga an yi zaben da za a fitar da sakamakon zabe ba domin ba’a yi zaben ba.

About andiya

Check Also

Eid-Al-Adha: Manna Group Greets Muslim Ummah, Urges Faithful to Imbibe Core Lessons

As the Muslim Ummah across the globe celebrates this year’s Eid-el-Kabir, the Manna Group Kaduna …

Leave a Reply

Your email address will not be published.