Home / Labarai / Hukumar Zabe Ta Dage Zabe A Kaduna

Hukumar Zabe Ta Dage Zabe A Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi
Hukumar Zaben kananan hukumomi ma8 zaman kanta a Jihar Kaduna ta sanar da dage zaben kananan hukumomi zuwa ranar 4 ga watan Satumba,2021.
Shugabar hukumar Dokta Saratu Binta Dikko – Audu ce ta sanar da hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin zaben, inda ta bayyana cewa sun sanar da dagewar ne ba a son ran su ba, sai domin hakan ya zama dole ba yadda za su yi.
Saratu Dikko ta kuma ce dalilin dagewar saboda rashin zuwan Batura be da za a yi amfani da su a wajen zaben, domin za a kawo su ne daga kasar Chaina, wato Baturan da Injunan zaben za su yi amfani da su.
Aaron yadda aka Sanya ranar zaben a can baya dai an shirya ne za a yi zaben a ranar 14 ga watan Agusta, 2021 sai ga shi kuma a halin yanzu an dage ranar, wanda kamar yadda shugabar hukumar ta bayyana cewa zai bayar da damar a kammala dukkan al’amuran gudanar da zaben domin a samu ingantaccen zabe.

About andiya

Check Also

TINUBU YA NADA GEORGE AKUME A MATSAYIN SAKATAREN GWAMNATIN TARAYYA

Daga Imrana Abdullahi Kamar dai yadda jaridar “Vanguard” ta rawaito cewa tun bayan rantsar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.