Home / Big News / Jihar Zamfara Ta Rasa Manyan Sakatarori Biyu

Jihar Zamfara Ta Rasa Manyan Sakatarori Biyu

 Imrana Abdullahi

Gwamnatin Jihar Zamfara ta rasa wadansu mutane biyu masu matsayin manyan sakatarori sakamakon dan takaitaccen Ciwo.

Manyan sakatarorin sun hada da Alhaji Yawale Dango, wanda ke aiki a ofishin shugaban ma’aikatan Jihar sa Alhaji Ahmed Sale, da ke aiki a ma’aikatar gidaje da bunkasa yankunan karkara.

Sale dai ya mutu ne ranar Talata shi kuma Dango ya mutu ranar Laraba.

Tuni dai aka yi Jana’izar su kamar yadda addinin musulunci ya shimfida.

Da yake aikewa da sakon gaisawar ta aziyya Gwamnan Jihar Zamfara ta hannun mai taimaka masa na musamman a kan harkokin kafafen yada labarai Alhaji Zailani Baffa, ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa mamatan ya kuma ba iyalansu hakurin jure rashin.

Matawalle ya kuma bayyana mamatan a matsayin mutane da ke aiki tukuru da suka sadaukar da kawunansu wajen yi wa Jihar Zamfara aiki.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.