Home / News / Korar Malaman Makaranta A Kaduna An Kalubalanci Sanata Uba Sani

Korar Malaman Makaranta A Kaduna An Kalubalanci Sanata Uba Sani

Kwamitin da ke fafutukar Yakin neman zaben dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna Isa Ashiru Kudan ya kalubalanci Sanata Uba Sani na APC sakamakon kasa yin maganar da ya yi game da lamarin korar malaman makaranta a Jihar Kaduna.
A cikin wata takardar da kwamitin Isa Ashiru ya fitar da aka rabawa manema labarai, kwamitin ya kalubalanci Uba Sani bisa yin shuru ya yi Gum da bakinsa yaki cewa komai a game da lamarin korar malaman makaranta da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi duk da cewa shi ne dan takarar Gwamna na  jam’iyyar APC a Jihar Kaduna.
Takardar mai dauke da sa hannun Daraktan fadakarwa da yayata manufofin dan takarar Gwamna Isa Ashiru, Yakubu Lere El – Saed, ya Sanya wa hannu ta bayyana cewa malaman makaranta sama da dubu biyu aka sallama a Jihar Kaduna kwanan nan.
Lere ya ci gaba da cewa ana kuma shirin yin Rusau a kasuwar Gwari da ke unguwar Rigasa da kasuwar garin Saminaka a karamar hukumar Lere.
“Saboda haka ne muke ganin yin shuru da Sanata Uba Sani ya yi wata alamace da ke nunin cewa zai ci gaba da aiwatar da ayyuka irin wannan da El – Rufa’I take yi, wanda mai yuwuwa ne takensa shi ne ci gaba da aikin da Gwamna El – Rufa’I ke aiwatarwa.
“Hakika ya dace kowa ya Sani cewa wannan kokari ne na ganin bayan ci gaban ilimin Firamare a Jihar Kaduna. Saboda alkalumman da ake da su game da batun harkar ilimi na tabbatar da cewa komai ya lalace idan aka yi la’akari da takardar kammala karatu domin akwai koma baya kwarai a zamanin mulkin Gwamna Nasiru El- Rufa’I, domin mutum zai yi ta tunanin cewa shin wai me take son cimma wa da irin wannan aikin na korar Malaman makaranta?
“Muna tausayawa wadanda wannan lamarin korar malaman makaranta ya shafa wato jama’ar Jihar Kaduna, malaman makarantu da kuma kungiyar NUT sakamakon kashe harkar ilimi baki daya a Jihar da wannan ne muke kokarin tabbatar maku cewa idan Honarabul Isa Ashiru Ashiru samu nasarar zama Gwamnan Jihar Kaduna za a yi maganin irin wannan kuma a inganta lamarin ilimin a Jiha baki daya.
“Muna kira tare da ba su hakurin cewa su bar komai ga Allah kuma muna kira a gare su da su tabbatar kowa ya yi rajista domin ganin bayan irin wadannan abubuwan na Gwamnatin APC a Jihar”, Cewar Daraktan wamitin Yakin neman zaben Isa Ashiru.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.