Home / MUKALA / KUNGIYAR AYCF TA GARGADI GWAMNONIN AREWA

KUNGIYAR AYCF TA GARGADI GWAMNONIN AREWA

TARON MANEMA LABARAI DA KUNGIYAR TUNTUBA TA MATASAN AREWACIN NAJERIYA ( AYCF) SUKA YI A GAME DA CECE – KUCEN DA AKE YI KAN YANCIN YANKIN NA SHIGA HARKOKIN DIMOKURADIYYA A 2023.
Mun kasance masu yin duba na tsanaki misamman a harkar batun kabilanci a tsarin Dimokuradiyya daga wasu Gwamnonin arewacin kasar guda Goma sha daya (11) da suka kasance suna ta yin cece – kuce game da batun yancin yankin na samar da shugaban kasa inda suke ta batun cewa a kai kujerar shugabanci Kudancin kasar.
Mun kasance cikin damuwa duk da gazawarsu na ceton yankin daga matsanancin talauci da yake fama da shi, matsalar yan Ta’adda Ta’adda satar jama’a ana neman kudin fansa, sai ga su suna ta yawon kokarin hana yankin zaben mutumin da ya dace ya zama shugaban kasa a nan gaba daga yankin Arewa. Saboda haka muna kyautata zaton cewa masu zaben dan takara da ake kira deliget ba za su bi irin son zuciyar da wadannan mutane ke da ita ba, wajen kokarin cimma manufarsu.
A matsayin mu na kungiya da muka amince da tsarin Dimokuradiyya, muna ganin ya zamar mana wajibi inda har muke yin kira ga wadannan Gwamnonin na Arewa. Kuma muna saran za su fahimci wannan;
1. Wannan ba dimokuradiyya bace ace wai shugabancin kasar nan sai daga kudanci zai fito a zaben 2023 saboda yancin masu zabe ne da su zabi mutumin da ya fito daga Kudancin Najeriya ko arewacin kasar. Saboda haka Talakawa na su magantu ba har yanzu don haka muke ganin ya zama karfa karfa ne ace sai dan takarar da ya fito daga Kudancin kasa ne zai yi takara.
2. Su wadannan Gwamnonin Arewa gida 11 ba su nuna cewa sun yi wani kokarin tuntubar mutanen yankin ba, Kafin su fitar da matsayar da cimma cimma na goyon bayan wani dan takara daga Kudancin Najeriya. Abu mai muhimmanci a tsarin Dimokuradiyya, shi ne tuntubar Talakawa ayi shawara da su, wannan ita ce tambaya mai muhimmanci musamman idan su wadannan Gwamnonin sun ce ra’ayin jama’a ne abin da ya fi muhimmanci.
3. Idan aka yi duba da irin yadda lamarin ya gudana a halin yanzu za a iya fahimtar cewa abu ne a fili ga yan Arewa masu yin zabe cewa an tursasawa zuciyarsu amincewa da son ra’ ain’t wadansu mutane yan siyasa marasa kunya da ke da wata manufa ta mikawa wani yanki mulki haka kawai, kamar dai irin yadda sojoji ke yi ya zamanin da ya wuce.
4. Hakika muna da masaniyar irin kokari da jajircewa da magabatan mu suka yi kamar su Sa Ahmadu Bello Sardauna da suka yi wa yankin aiki saboda haka a halin yanzu ba mu mamaki ba idan an yi wa kokarin nasa kafar Ungulu domin kawai son ran wadansu mutane da suka kasance Gwamnoni. Don haka abin damuwa ne cewa Gwamnonin mu sun sayar da mu a wannan lokacin, ta hanyar hana Talakawa zaben abin da ya dace da su.
5. Mun samu damuwa kwarai irin matakin da muke yi na samun sababbin jini a kan madafun iko musamman a fannin tsarin Dimokuradiyya a halin yanzu an kashe shi da gangan sakamakon aikin Gwamnoni masu son zuciya daga yankin arewacin kasa.
6. Manufar wadannan Gwamnonin ta gaskiya da a halin yanzu suka boye shi ne su yi wa shugaba Buhari yarfe a kokarin aiwatar da son zuciyarsu. Sun yi tsammanin Buhari da yake son mutanensa kwarai ya juya baya kawai su kutso da wanda suke bukata ta bayan gida. Saboda haka ne muke bayar da shawara ga Muhammadu Buhari da kada ya amince da abin da wadannan mutanen ke bukata a sayar da yancin mutanen mu a hana su zaben wanda suke bukata da ya kasance dan Arewa ko akasin hakan.
7. Saboda haka muna yin kira ga dukkan yan Arewa da ke da kyakkyawan tunani da kada su amince da wannan kokarin son zuciyar da wasu ke bukatar aiwatarwa duk da cewa kundin tsarin mulki ya Dora Dora alhakin kare martaba da mutuncin wadannan mutane da ake yi wa  jagoranci. Saboda haka muke fadi da babbar murya cewa ba zamu amince da wannan karfa karfar ba da sunan Dimokuradiyya.
8. Saboda haka muke kara daga murya da yin kira ga shugaba Bihati da kada ya bari yankin Arewa ya rushe domin muna saran cewa masu zabe za su yi abin da ya dace da ke da alhakin kare martaba da mutuncin Arewa da a halin yanzu ake saran su fitarwa da yankin kitse a wuta su Kato yankin kenan.
9. Muna kuma kara fadakar da jama’a cewa muna sa idanu sosai a game da irin abin da wadannan mutanen ke aiwatarwa duk da Mutanensu ba su bukatar abin da suke yi, domin kawai bukatarsu ta biya saboda haka muna jiran ganin abin da zai faru Gobe, ko sun san abin da ake nufi da tsarin dimikuradiyya da ba kowa yancinsa.
Sa hannu
Alhaji Yerima Shettima
Shugaba na kasa
A madadin AYCF

About andiya

Check Also

Sanata Aminu Waziri Tambuwal Jagora Ne Abin Koyi –  Atiku Yabo

  Sakamakon irin Nagarta da kokarin aiwatar da ayyuka domin ci gaban  jama’ a yasa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.