Home / News / SAI AN ILMANTAR DA YAN JAM’IYYA SOSAI – YARIMAN BAKURA

SAI AN ILMANTAR DA YAN JAM’IYYA SOSAI – YARIMAN BAKURA

 

IMRANA ABDULLAHI

Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayyana cewa babban aikin da ke gaban kowa ce jam’iyya shi ne bayar da ingantaccen ilimin me ake nufi da siyasa da kuma matsayin yan jam’iyya a koda yaushe a cikin jam’iyyar.

Ahmad Sani Yarima ya ce a mafi yawan lokuta zaka ga yayan jam’iyya ba su iya biyan kudin da ya dace su biya na kasancewarsu yayan jam’iyyar sai lokacin da mutum ke son tsayawa takara kawai sannan ya hada dukkan kudin karo karo na jam’iyya ya biya lokaci guda domin kawai ya na son tsayawa takara.

Sanata Ahmad Sani Yarima ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin gidan Talbijin na kasa NTA mai suna “Tuesday Live” a ranar Talata.

Yarima ya ci gaba da cewa ” ya na da kyau yayan jam’iyya su san irin hakkin da ke kansu na taimakawa jam’iyyar da suke ciki domin gujewa matsalar bayar da makudan kudi idan ana son yayan jam’iyya su zabi wani ko wasu yan takarar da za su tsaya neman zabe su zama wakilai ko shugabantar al’ummar kasa”.

Binciken da wakilin mu ya gudanar ya nuna cewa a can shekarun baya da suka gabata yayan jam’iyya ne ke tafiyar da lamuran jam’iyyarsu ta hanyar biyan kudin ka’ida kamar yadda yake a kunshe a kundin tsarin jam’iyya musamman a lokacin PRP da dai sauransu.

Amma a yanzu lamari ya canza saboda dan takara ne ke sayen masu zaben fitar da dan takarar jam’iyya da makudan kudi da nufin ya tsayawa jam’iyyarsu takara.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.