Home / News / Kungiyar Marubuta Labarin Wasanni Sun Zabi Isiah Benjamin shugaba Da Jocob Dickson Sakatare

Kungiyar Marubuta Labarin Wasanni Sun Zabi Isiah Benjamin shugaba Da Jocob Dickson Sakatare

Kungiyar Marubuta Labarin Wasanni Sun Zabi Isiah Benjamin shugaba Da Jocob Dickson Sakatare
Imrana Abdullahi
Kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Jihar Kaduna sun zabi sababbin shugabannin da za su ja ragamar shugabancin kungiyar.
An dai sake zaben Kwamared Isiah Kemje Benjamin da Okpani Jocob Onjewu Dickson a matsayin shugaba da sakatare inda za su ci gaba da jan ragama a tsawon shekaru uku masu zuwa nan gaba.
Sababbin shugabannin da aka kaddamar sun hada da Kwamared Isiah Benjamin wakilin jaridar Leadership a Jihar Kaduna a matsayin shugaba, Dhehu Usman Abdullahi na gidan rediyon Nagarta a matsayin mataimakin shugaba, Okpani Jocob Onjewu Dickson na jaridar New Nigeria, Sakatare sai Abimaje Moses na gidan Talbijin na AIT mataimakin Sakataren kungiyar marubuta labarin wasanni.
Sauran sun hada da Stella Kabruk Solomon ta kamfanin Dillancin labaran Nijeria, matsayin jami’ar kula da walwalar jama’a, Dari Idris na gidan rediyon tarayya Sakataren kudi sai kuma Mike James na jaridar Desert Herald a matsayin ma’ajin kungiyar.
An dai yi taron kaddamar da sababbin shugabannin kungiyar ne a ranar Lahadi da ta gabata 14 ha watan Fabrairu, 2021 a filin wasa na  Sardauna Ahmadu Bello Kaduna karkashin jagorancin Josep Jide Bodunde inda ya aka samu halartar manyan baki da dama da suka hada da manyan masu ruwa da tsaki a hidimar harkokin wasanni a Jihar duk bisa sa idanun mataimakin shugaban shiyyar Arewa maso Yamma Malikawa Idris.
Kamar yadda shugaban kwamitin zaben ya bayyana “Bayan kammala aikin tantancewar da aka yi cikin nasara na yan takara daban daban domin su shugabanci kungiyar ta marubuta labarin wasanni ta kasa reshen Jihar Kaduna a shekarar 2021, ba tare da samun wata turjiya ko korafi ba, don haka yan takarar sun tabbata an sake zabensu ba da hamayya ba”.
Sauran mambobin na SWANECO da suka gudanar da zaben duk yan takarar sun kasance babu wata hamayya, sun kuma hada da Nonye Juliet Ekwenugo Sakatare da Ibrahim Dahiru Danfulani.
A jawabinsa na karbar ragamar shugabancin, Kwamared Isiah bayar da tabbaci ya yi cewa a koda yaushe zai gudanar da shugabancin da zai rungumi kowa da kowa domin samun nasarar harkokin wasanni a nan da tsawon shekaru uku masu zuwa.
Ya nada Josep Jide Bodunde da Zakari Haruna Isah a matsayin wadansu jigogin wannan tafiya ta kungiyar marubuta labarin wasanni.
Sai kuma Barista Abu Usman, da ya Rantsar Rantsar shugabannin da aka zaba.
Manyan bakin da suka halarci taron kaddamarwar sun hada da ko-odinetan shiyya a ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa shiyyar Arewa maso Yamma Alhaji Abdullahi Idris, shugaban FA na Jihar Kaduna, Alhaji Sharreef Alkassim, wanda ya samu wakilcin Alhaji Yusuf Best, sai mataimakin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa shiyyar arewa Alhaji Idris Malikawa da kuma sakataren shiyya na kungiyar marubuta labarin wasanni Alhaji Abdulkarim Aodu.
Sauran sun hada da sakataren tsare tsare na kasa a bangaren wasanni matasa (YSFON)I, sai mai taimakawa shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna na kashin kansa, Tasi’u Musa da kuma Manajan filin wasanni na Ahmadu Bello da ke Kaduna Mista Gideon Malo.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.