Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Matasan APC Za Su Kai Gwamnan Zamfara Kara Kotu

Kungiyar Matasan APC Za Su Kai Gwamnan Zamfara Kara Kotu

Kungiyar Matasan APC Za Su Kai Gwamnan Zamfara Kara Kotu
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta kasa karkashin jagorancin Dokta Suleiman Aliyu Shinkafi sun bayyana barazanar kai Gwamnan Jihar Zamfara kotun bunkasa kasashen Afrika in har ya kasa yi wa duniya bayani game da batun yin sulhu da yan bindiga a Jihar da yake yi wa jagoranci.
Dokta Suleiman Shinkafi ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai na kasa da kasa da ya kira a Kaduna.
Sokta Suleiman Shinkafi ya ce ta yaya ana ta batun wai ana yin sulhu da yan bindiga amma a kullum sai kashe mutane ake ta yi dare da rana, wannan wane irin sulhu ne.
“Saboda haka mu matasan jam’iyyar APC mun ba Gwamnan Zamfara Bello Mohammad Matawalle wa’adin kwanakin sati biyu da ya yi wa jama’a bayani game da wannan lamari na sulhu, in ba haka ba kuma za mu kai shi kotun bunkasa yankin Afrika domin nemawa jama’ar Jihar Zamfara yancinsu”.
Dokta Shinkafi ya kara da cewa su na sane da cewa fa tun asali ba kuri’a bace ta kai Gwamna Matawalle ga kujerar Gwamnan Zamfara kawai wani tsari ne na shari’a da ta ba jam’iyyar PDP kasancewa ita ce ta biyu a zaben Gwamnan Jihar Zamfara lokacin da ya gudana can baya”.
Dokta Suleiman Shinkafi ya kuma fito fili ya bayyana cewa su na goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Abdul’Aziz Yari Shetiman Mafara da ya zama shugaban Jam’iyyar APC na kasa kasancewarsa mutum ne mai jajircewa wajen ayyukan jam’iyya kuma shi ne mutumin da bai ta ba canza sheka ba ya koma wani gefe na daban, don haka su a matsayinsu na matasa suka yanke hukunci bayan taronsu cewa su na goyon bayansa ya zama shugaban APC na kasa.
“Ko a kwanan na tsohon Gwamna Abdul’Aziz Yari ya tabbatar da cewa shi ne shugaba kuma jagoran APC a Jihar Zamfara domin irin yadda ya taimakawa mutane da abin hannunsa domin su samu damar yin Azumi a cikin walwala wani abin jindadi ne da za a yi alfahari da shi.
“Saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnan Zamfara da ke kokarin komawa APC da cewa ya Sani idan ya koma APC zai zo ne a matsayinsa na dan jam’iyya kawai domin shi emti ne amma ba shugaban APC, shugaban APC shi ne Abdul’Aziz kamar yadda kowa ya sani”.
Hakazalika matasan na APC sun yi kira ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Ahmad Sani Yariman Bakura da ya tsaya a waje daya in APC zai yi ya tsaya a nan, in kuma PDP zai yi nan ma ya tsaya ya yi PDP amma ba kamar yadda a yanzu kowa ya rasa inda ya dosa ba.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.