Home / KUNGIYOYI / KUNGIYOYI 102 SUN SAYAWA GWAMNA MATAWALLE FOM DIN TSAYA WA TAKARAR GWAMNAN ZAMFARA KARO NA BIYU

KUNGIYOYI 102 SUN SAYAWA GWAMNA MATAWALLE FOM DIN TSAYA WA TAKARAR GWAMNAN ZAMFARA KARO NA BIYU

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
Sakamakon nuna yarda da kuma gamsuwa da jagorancin Honarabul  Dokta Bello Muhammad Matawallen Maradun, Kimanin kungiyoyin 102 a Jihar Zamfara suka yi karo-karo suka tara naira miliyan 50 domin saya ma Gwamnan fom din takarar gwamna Karo na biyu a 2023.
A cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar APC reshen Jihar ZamfaraYusuf Idris Gusau, da aka rabawa manema labarai.
Saboda haka ne jam’iyar Apc ta Jihar Zamfara ke gayyatar dukkanin halatattun yayan jam’iyar APC na jihar zuwa wajen gangamin gabatar da Cekin kudi ga mai daraja Gwamnan Jihar Zamfara Honarabul Dokta  Bello Muhammad Matawallen Maradun karkashin jagorancin Shugaban jam’iyar APC na iharJ Zamfara Honarabul Tukur Umar Danfulani.
Za a hadu a Babban Masallacin idi da ke Tudun Wada Gusau da karfe 8:00 na safe ranar Jumu’a 6/5/2022 inda za a taka zuwa Fadar gwamnatin jihar domin mika Cekin kudin ga Gwamnan.
Shugaban jam’iyar na kara nuna godiyarsa ga Allah da al’ummar jihar Zamfara akan irin Soyayya da su ke nunawa gwamnatinsu tare da rokonsu da su cigaba da baiwa gwamnatin goyon baya.
Haka zalika Shugaban ya nuna matukar godiyarsa ga wadannan kungiyoyin da sauran magoya bayan wannan gwamnatin tare da tabbatar da masu da cewa jam’iyar Apc ba za ta taba yar da su ba
5th May, 2022

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.