Home / MUKALA / Magatakardan Kwalejin Ilimin Gwamnatin Tarayya Ya Yi Amfani Da Ofishinsa Wajen Daukar Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Jihar Katsina

Magatakardan Kwalejin Ilimin Gwamnatin Tarayya Ya Yi Amfani Da Ofishinsa Wajen Daukar Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Jihar Katsina

Magatakardan Kwalejin Ilimin Gwamnatin tarayya da ke Katsina Garba Isyaku Dantunture a bayyana cewa a lokacin shugabancinsa ya dauki mutane aiki ba tare da ya sansu ba sai dai uyayensu kawai ya Sani.
Ya kuma ce ya dauki a kalla mutane 20 saga Jihar Gombe duk kuma bai san su ba sai ta dalilin uyayensu.
Ya bayyana a cikin hirar da ya yi ta wayar tarho da hirar ta watsu a kafafen Sada zumunta na zamani da wato ( social media)
Kamar yadda magatakardan ya ce in dai batun daukar aiki ne ( Provost) bai ja da shi kawai sai dai a aiwatar da abin da ya ce kawai.
Magatakardan  Kwalejin horas da Dalibai ta Gwamnatin Tarayya da ke Katsina Garba Isyaku Dantunture, ya ce an yi amfani da mai kula da harkokin kudi na makarantar wato ( Burser) ya yi amfani da sama da miliyan Arba’in domin ya samu nasara  a kotu bisa korarsa da aka yi.
Ya bayyana hakan ne ta hirar da ya yi da wani ta wayar tangaraho wadda ya bazu a kafar Sada zumunta ta yanar Gizo, Sato ( Social Media).
Garba Isyaku ya yi maganganu da dama da suka hada da cin mutunci da kuma neman janyo rikici da damar ma’aikata ba tare da bin ka’idoji ba.
Ga dai wadansu batutuwa da Garba Isyaku Dantunture ya bayyana a cikin tattaunawarsu har karo uku.
HARSASHIN SABBIN KASHE KASHE A KARAMAR HUKUMAR KAFUR TA JIHAR KATSINA.
 
 
 
Sabon rikicin siyasa da ta’addanci ya kunno kai a Karamar Hukumar Kafur da ke Jihar Katsina, Hakan ya bayyana ne a cikin bayanin a wasu faya-fayen munanan maganganu da Hukumomin Tsaron Jihar Katsina suka samu a inda Magatakardan Babbar Kwalejin Ilimi Gwamnatin Tarraya (FCE) da ke Katsina Garba Isiyaku Dantuture ya yi.
 
 
 
Ga wasu daga cikin ikirarin batanci da tanajin fitina wanda Garba Isiyaku Dantuture ya yi:
 
 
 
1, Shirya taro a asirce ba tare da izinin hukuma ba, kuma a lokacin da Gwamnatocin Tarraya da na Katsina suka hana tarurruka.
 
 
 
2, Halartar taro da makamai don tallafawa kansa.
 
 
 
3, Yin rantsuwa da shan alwashin sai ya haddasa rikicin da za’a kashe fiye da mutane  100 domin cimma burin kashin kansa.
 
 
 
4, Horas da ‘yan ta’adda da saya masu muggan haramtattun makamai da ba su umurnin su kashe duk wadanda ba su yarda da ra’ayi irin nasa ba.
 
 
 
5, Bugun kirjin zai yi amfani da jahilcin al’ummarsa domin tada babban fitina da zai janyo kashe kashen mutane a Yankin Daneji, a inda nan ne mahaifarsa.
 
 
 
6, Yin taro da matasan garin Dankanjiba da ba da umurnin a kashe Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Kafur Hon. Garba Hussaini Dankanjiba, wanda shi haifaffen garin ne.
 
 
 
7, Ba da umurnin a kashe Alhaji Bello Kagara wani babban mai fada, aji aminin Mai Girma Gwamna Jihar Katsina  kuma Darakta a Gwamnatin Tarraya.
 
 
 
8, Daukar alkawarin kallubalantar da Gwamna Aminu Bello Masari da kawar das hi mudin ya neme ya tsare masa gaba.
 
 
 
9, Daura damarar korar duk  ‘yan siyasar da ke yankinsa da Karamar Hukumar Kafur.
 
 
 
10, Fitowa karara ya ce baya kaunar duk wani dan siyasa da ke Karamar Hukumar Kafur’, Wanda hakan ya sanya ba ya hurda da ko daya daga cikinsu.
 
 
 
11, Yin amfani da offishinsa domin dauka da horas da ‘yan ta’a’ddanci a fakaice a Yankin Daneji.
 
 
 
12, Daukar nauyin kai ziyarar mako -mako a yankin Daneji domin horas da matasa yan juyin juya hali.
 
 
 
13, Yin miyagun maganganu da tsinuwa ga dukkan manyan Karamar Hukumar Kafur da nada kansa sabon jagoran juyin juya hali a wannan karamar hukumar.
 
 
 
14, Sayawa da horas da matasa fiye da dari biyu a tashin farko tabar wi-wi da kaisu filin taro domin aikin ta’adanci.
 
 
 
15, Kama sunan Mai Girma Sanata Muhammadu Danjuma Goje, Tsohon Gwamnan Jihar Gombe karara a matsayin wanda ya horas da shi wajen ta’a’dancin da kisan bayin Allah.
 
 
 
Kafin aji ta’asar da mugun shirin Garba Isyaku Dantuture sai dai ya zama wajibi, kuma hakki ne akanmu mu yi kira ga jama’a a matakin Karamar Hukumar, da Jihar Katsina dana Tarayya su dauki babban mataki a kan wannan batu, musamman idan aka yi la’akari da irin mawuyacin halin tsaro da Jihar Katsina take ciki.
 
 
 
Kada ayi shirin ta leko ta koma yayin da Jihar Katsina ta hango sauki ta hanyar daukin da Gwamnatin Tarayya ta kai mata, akwai tashin hankali a samu shirin aikin aika aika don kurum cimma burinsa.
 
 
 
Bayan wannan , akwai bukatar tsauraran matakai don kare rayuwar mutanen wannan Karamar Hukumar daga sharrin wannan masharrancin ma’aikaci.
 
 
 
Babbar maganar itace, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya,  a karkashin Ministan Ilimi, Mal. Adamu Adamu da hukumar FCE Katsina da su saurari kalaman Magatakarda Garba Dantuture domin nazarin hadarin da ke tattare da zamansa a tsakiyar dalibai yara a babbar makaranta irin wannan inda ake horar da dalibai kuma malamai.
 
 
 
 Don haka muna kira da a dubi hanyoyin da ya bi ya zakulu yaran da yake ikirarin ya dauka aiki. Shin an bi ka’idojin daukar aiki? Koko kamar yadda yake ikirari shi kadai ke da ikon daukar ma’aikata a wannan makaranta.
 
 
 
Muna kuma kira da babbar murya a dauki wadannan matakai don kare wannan makaranta, Jihar Katsina da ma kasa Nigeria baki daya.
 
 
 
Ya kamata hukumar EFCC ta binciki kalamunsa na barnar kudi sama da naira miliyan 40 a makaranta irin wannan a lokacin shari’ar korarsa da aka yi. 
 
 
 
Kira na karshe shi ne, kungiyoyin Wayarda Kan Jama’a masu zaman kansu CSO su tashi tsaye don ganin an kare al’ummar wannan Karamar Hukumar da wannan makaranta daga sharrin wannan dan ta’a’dda.
 
 
Bincikenmu ya nuna cewa tarihi ne yake maimaita  kansa domin hukumar wannan makaranta ta taba korarsa bisa laifuffuka masu kama da wadannan.
 
Ku saurari Garba Isyaku Dantuture da bakinsa.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.