Home / News / Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

 

…Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu

 

Bashir Bello majalisar Abuja

Honarabul Alhassan Ado Doguwa ya bayyana tsarin majalisa a Dimokuradiyya a matsayin abin da ya bambanta da mulkin Karfa karfa.

Ado Doguwa ya ce ko tsarin mulkin soja ake hakika shima babu Dimokuradiyya a cikidon haka tsarin majalisa wuri ne da ya hada dukkannin yan kasa a wuri daya kasancewar majalisa wakilai ne na yan kasa da ke da wakilci daga ko’ina a Najeriya baki daya.

Alhassan Ado Doguwa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

A majalisa ne ake tattauna ayyukanta tare da makomar mutanen kasa baki daya, don haka ya fuskar ci gaba akwai kyawawan misalai da aka yi da suka hada da aikin tagwayen hanyar da ta tashi daga Kano zuwa Maiduguri da aka fara tun lokacin mulkin Obasanjo da a yanzu ta zama tarihi sai kuma aikin titi mai hanyoyi biyu biyu daga Abuja, Kaduna zuwa Kano da a lokacin shugabancin Muhammadu Buhari aka yi da dai wadansu ayyuka da dama da wadanda aka fara a lokacin mulkin Goodluck Buhari ya kaddamar da kammala aikin da dai sauransu da dama duk abubuwa ne da ake yi domin kasa ta ci gaba

” Duk da irin wannan bai hana ba a matsayin mu na wakilan jama’a mu fadi wadansu bangarori ko sassan da muke gani akwai gazawa a bangaren Gwamnati ba, gazawan nan a ganina ba gazawa ce ta Bola Ahmed Tinubu a yau ba, ba kuma gazawa ce ta Muhammadu Buhari a jiya ba, ba kuma gazawa ce ta tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan a shekaranjiya ba ko ta marigayi Umaru Musa da ya gabata ba duk gazawa ce ta tsarin da ake ciki wato ( system) don haka akwai dimbin kalubalen da sai an cire ra’ayi na siyasa an cire ra’ayi na maganar kabilanci an yarda matsalolin da ke fuskantar kasa an amince na al’umma ne baki daya, da suka hada da matsalar rashin ingantaccen ilimi musamman a kauyuka baki daya da harkar samar da lafiya a matakin farko da kuma sace – sacen mutane duk wadansu abubuwa ne da yakamata Gwamnati ta kara yin kaimi wajen magance su hakan ya sa mu a matsayin wakilan jama’a muke yi wa Gwamnati kaimi a kara tabbatar da an samo hanyar da za ta yi maganin tashe tashen hankulan nan musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. Saboda haka ne muna cikin wakilcin da shugaban majalisa ya bayar da za mu hadu da kungiyar tuntuba ta arewa ( Arewa Consultative Forum) muga shugaban kasa idan Allah ya yarda kuma daya daga cikin dalilin hakan shi ne muga yadda za a cire wannan tarnakin matsalar tsaro a tsakanin al’ummar mu”.

Wani abu kuma da ya dace “in sarawa Gwamnatin tarayya a yau kuma in yi wa shugaba Tinubu godiya shi ne yunkurin da ya yi na ba ministan shari’a damar ya je ya yi karar Gwamnonin Jihohi Kan meye fassara a game da matsayin kananan hukumomi kuma kotun koli ta kasa ta yi hukunci a kan tsarin mulkin Najeriya na Gwamnatocin kananan hukumomi kamata ya yi su zama masu cin gashin kansu ta yadda za a rika ba su kudinsu kai tsaye ba sai ya shiga cikin hannun wani ba don haka ina tabbatar maka idan shugaban kasa ya yi nasarar hakan a kotun koli ina tabbatar maka mu a majalisa za mu goyi bayan hakan domin ta hakan ne kawai za a yi maganin rashin tsaro, ingantaccen ilimi da harkar lafiya matakin farko amma a dinga bayar da kudin da ya dace a ce suna zuwa hannun kananan hukumomi kawai su rika fadawa a hannun Gwamnatocin Jiha kuma da yawansu ayyukan da ake yi da kudin ba ayyukan kananan hukumomin ake yi da su ba don haka ya dace yan Najeriya su sarawa shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan hakan matakin da ya dauka na cirewa yan Najeriya dabaibayin da yake lankwame kudinsu na kananan hukumomi. Kuma a bangaren majalisa dattawa kun ji kudirin doka da ya taso kuma a bangaren majalisar wakilai mu muna shirye mu yarda mu amince da abin cewa ma zaben kananan hukumomi ma ya dace a dawo da shi hannun hurumin hukumar zabe ta kasa domin in har ba a rika yin zaben kananan hukumomi daga mataki na kasa baki daya ba to, shugabannin kananan hukumomi da kansilolinsu za su ci gaba da zama yan kamshin shata ne na gwamna da yake busa usur ya nada na nadawa kamar yadda ka san ya na nada kwamishinoni kawai haka yake nada shugabannin kananan hukumomi don haka in aka ba hukumar zabe ta kasa dama to zaka ga wani abu mai kama da abin da ka gani a zauren majalisa kaga Sanatan APC, PDP? Jam’iyyar Lebo ga sunan dai kala kala wani ma Sanatan har da Jar hula a kansa kuma duk Dimokuradiyya ce ta bayar da dama a yi hakan idan ana son ayi zabe na kirki a kananan hukumomi dole ne ka ba hukumar zabe ta kasa aikin

Kaga dai an samu abubuwa tagwaye guda biyu inda su a majalisar Dattawa ta kasa suka ce a ba su yancinsu mu kuma a nan muka ce wato a majalisar wakilai a ba hukumar zabe damar yin zaben kananan hukumomi wanda duk hakan zaka ga cewa Dimokuradiyya ce ta kawo su saboda haka ne muke yin kira ga yan jarida da su bayar da gudunmawa wajen wayar da kan al’umma a samu gyara Najeriya ta yi kyau ta kara inganta sosai, in kuwa aka samu cikas to da ni da gwamnati da duk yan jarida za a yi mana dariya a kan mun gaza, muna kuma fatan Allah jada ya kawo wannan ranar da za a yi wa shugabanni, gwamnati ko mu dariyar mun gaza.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.