Home / News / Majalisa Za Ta Mara Wa INEC Baya Don Gudanar Da Ingataccen Zabe A 2023 — Ahmed Lawan

Majalisa Za Ta Mara Wa INEC Baya Don Gudanar Da Ingataccen Zabe A 2023 — Ahmed Lawan

Majalisa Za Ta Mara Wa INEC Baya Don Gudanar Da Ingataccen Zabe A 2023 — Ahmed Lawan

 

 

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bada tabbacin cewa majalisar dokoki ta tarayya za ta bada dukkan goyon bayan da ake bukata ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC wajen samar da kyakykyawan yanayi da zai tabbatar da gudanar da ingantaccen zabe a shekarar 2023.

 

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Ezrel TABIOWO, MBSC, Fsca Mai taimakama shugaban majalisar dattawa a kan aikin jarida da aka rabawa manema labarai.

 

 

Lawan ya bayyana haka ne ranar Talata a yayin da yake jawabi a wajen taro tsakanin kwamitin majalisar na hadin gwiwa a kan zabe da hukumar zabeb a Abuja.

 

 

Lawan ya jaddada bukatar kirkiro karin runfunan zabe domin samar da tsaro ga masu zabe da kakyakwan wuraren zabe a Najeriya.

Karin yawan rumfunan zabe a duk fadin kasar nan, a cewar sa, zai kawo sauki ga masu jefa kuri’a da basu damar kada kuri’ar su lokacin zabe.

Ya bada tabbaci ga INEC da yan Najeriya cewa majalisar zata ba hukumar zaben cikakken goyon baya don ganin an samu kyakykyawan yanayin zabe ga yan Najeriya.

Yayin da yake jaddada bukatar karin yawan yan Najeriya wajen kada kuri’a, shugaban majalisar yayi kira ga yan siyasa, jama’iyyu da kungiyoyin sa kai na farar hula da su fadakar da yan kasa masu rijistar zabe a yayin da ake tunkarar zaben 2023.

A cewar sa, tattara karin masu rijista domin yin zabe zai habaka tsarin zabe a kasar nan bayaga kirkiro karin rumfunan zabe.

A jawabin sa, shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu yace an kafa rumfunan zabe 119,973 da ake amfani da su a yau tun a shekarar 1996.

Yace matsalar zuwa rumfar zabe ga masu jefa kuri’a tana da gaggarumar illa ga ingancin zabe da ma dimokaradiyya kanta a Najeriya.

 

 

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.