Home / News / Hukumar Zaben  Jihar Kaduna Ta Dage Ranar Zaben Kananan Hukumomi

Hukumar Zaben  Jihar Kaduna Ta Dage Ranar Zaben Kananan Hukumomi

Hukumar Zaben  Jihar Kaduna Ta Dage Ranar Zaben Kananan Hukumomi
Mustapha Imrana Abdullahi
Hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar Kaduna ta dage lokacin gudanar da zaben da ta shirya yi a ranar 15 ga watan Mayu 2021 domin zaben shugabanni da Kansiloli a matakan Kananan hukumomin Jihar.
Mai rikon shugaban hukumar ta (KADSIECOM) Malam Ibrahim Sambo ne ya shaidawa manema labarai hakan a Kaduna.
Ibrahim Sambo, a wajen wani taron manema labarai da ya yi a ranar Laraba 3 ga watan Mayu 2021, a ofishin hukumar da ke Kaduna.
“An samar da wata sabuwar rana kamar yadda aka yanke shawara a hukumace cewa a yanzu za a yi zaben a ranar 5 ga watan Yuni 2021”, inji shi.
Ya ce a kwanan baya a lokacin wani taron manema labarai da aka yi a ranar 15 ga watan Fabrairu 2021, inda aka fitar da jadawalin ranar da za a yi zaben na kananan hukumomi, an samu korafe korafe da yawa daga masu ruwa da tsaki a harkar zabe inda kuma aka yi maganar a dage ranar zaben.
 “Gwamnatin Jihar Kaduna tuni ta samar da hukumar gudanarwar ita wannan hukuma ta zaben Jihar Kaduna inda aka Rantsar da su a ranar 2 ga ha watan Mayu 2021.
” Saboda shi lamarin zabe abu ne mai tafiya da lokaci, don haka muka hadu a matakin hukumar zaben a jiya kuma mun cimma matsaya, don haka ne muka kira domin shaida maku irin yadda lamarin zai kasance”, inji Ibrahim Sambo.
“Ranakun da aka rasa a wancan lokacin da aka sanar su ne kwanaki 16, don haka ne muka zauna kuma mun tattauna batun inda muka yanke hukuncin cewa a a dai- daita kwankin domin lissafi ya kama Sambel sosai, saboda hukumar zaben Jihar Kaduna na bukatar yin aikin da ya dace”, inji shi.
  Kamar yadda ya bayyana cewa bisa irin yadda aka fitar da jadawalin zaben a yau an fara gudanar da shirye shirye kenan wato daga 3 ga watan Mayu kamar yadda doka ta tanadar, saboda ya dace a bayar da kwanaki Casa’in (90) amma da wannan tsarin an ma bayar da kwanaki 93 kenan.
“Zaku ta fi da kwafin dokoki gida biyu ta zaben kananan hukumomi,  dokar hukumar zabe ta Jiha (SIECOM) da dokar kananan hukumomi” kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa daga ranar 10 ga watan Afrilu zuwa 10 ha watan Mayu, an bayar da izini ga jam’iyyun siyasa su gudanar da zaben fitar da Gwani.
Sai “Litinin 29 ga watan Mayi rana ce ta karbar fom din tsayawa takara. Sai kuma ranar 12 ga watan Mayu a mayar da fom din tsayawa takara”.
“Litinin 17 ga watan Mayu zuwa 19 Laraba a tantance takardun tsayawa takarar da aka cika wannan kuma hukumar zaben ce za ta yi hakan
“Ranar Litinin 24 ga watan Mayu ce rana ta karshe domin mayar da fom kuma ita ce ranar biyan kudin da ba za a mayarwa mutum ba”.
Sai kuma ranar “29 ga watan Mayu ta zama ranar karshe ga dukkan dan takarar da ke son jamyewa idan ya fasa tsayawa takara”, Ibrahim ya jaddada hakan.

About andiya

Check Also

I Want To Assist My People – Barister Abubakar Ahmad Muhammad

FROM IMRANA ABDULLAHI KATSINA All progressive congress (APC) candidate that is hoping to represent Funtua/ …

Leave a Reply

Your email address will not be published.