Home / News / Majalisar Wakilai: Sani Jaji Zai Maye Gurbin Abbas Tajuddeen?

Majalisar Wakilai: Sani Jaji Zai Maye Gurbin Abbas Tajuddeen?

Daga Imrana Abdullahi
Kamar yadda wadansu bayanai suka bayyana a kafar yada labarai ta jaridar Leadership da ke da babban ofishinta a Abuja na bayanin cewa akwai yuwuwar shirin canza dan majalisar da jam’iyyar APC ke son ya zama shugaban majalisar wakilai ta kasa da tun farko jam’iyyar ta bayyana goyon bayan ta ga dan majalisar wakilai daga Jihar Kaduna mai wakiltar karamar hukumar Zariya Dokta Abbas Tajuddeen.
Kamar dai yadda bayanan ke nuna wa cewa akwai yuwuwar za a canza sunan Abbas Tajuddeen da na Honarabul Aminu Sani Jaji daga Jihar Zamfara domin ya zama shugaban majalisar wakilai ta Goma.
Ana ganin dai shi Aminu Sani Jaji na daga cikin yan majalisa shida masu neman wannan kujerar
Sai dai ana ganin cewa shi Abbas Tajuddeen da kuma Honarabul Wasai da suke neman kujerar za a saka masu da mukaman ministoci.
Idan dai hakan ta tabbata ana ganin hakan zai kawowa yunkurin da Sanata Abdul’Aziz Yari Abubakar yake yi na son zama shugaban majalisar Dattawa ta Goma, kasancewar Aminu Sani Jaji ya fito ne daga Jihar Zamfara kuma jam’iyyarsu daya ta APC.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.