Home / KUNGIYOYI / Manoma  Miliyan 15 Za Su Amfana Da Shirin Noman Zamani – Aliyu Waziri
Honarabul Aliyu Muhammad Waziri dan marayan zaki

Manoma  Miliyan 15 Za Su Amfana Da Shirin Noman Zamani – Aliyu Waziri

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Noman zamani ta kasa (NAMCS) Honarabul Aliyu Muhammad Waziri ya bayyana cewa a kalla mutane miliyan Goma Sha Biyar ne za su amfana da shirinsu na Noman zamani a duk fadin Nijeriya.
Shigaba Aliyu Waziri ya bayyana hakan ne lokacin da yake bayani ga manema labarai jim kadan bayan kaddamar da reshen shugabancin kungiyar na kasa reshen babban birnin tarayya Abuja.
Waziri ya ce hakika kungiyoyin gama kai za su amfana a duk fadin kananan hukumomin da ke Najeriya guda 774 inda kowace mutane 250 za su  amfana da shirin, musamman a bangaren Noman Kaji.
Ya ce wannan zai taimaki Gwamnati wajen samawa jama’a aikin yi da kuma rage radadin talauci ga kuma samar da wadataccen abinci ga kasa domin yan kasa har da baki.
“Saboda haka wannan mihimmiyar rana ce da ake kaddamar da reshen babban birnin tarayya Abuja, kananan hukumomi da suka hada da na shiyya domin ciyar da kasa gaba”, inji Aliyu Muhammad Waziri dan marayan Zaki.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.