Home / Labarai / Masari Ya Rufe Kasuwannin Jihar Katsina

Masari Ya Rufe Kasuwannin Jihar Katsina

Daga  Imrana Abdullahi
Sakamakon samun wani mutum guda dauke da kwayar cutar korona a garin Dutsinma, Gwamna Aminu Bello Masari ya bada umurnin a rufe karamar hukumar ta tun daga karfe bakwai na safiyar gobe Juma’a, 17 ga watan Afrilu 2020.
Gwamnan ya kuma bayar da umurnin a rufe dukkan manyan kasuwanni  masu ci sati-sati da suka hada da Mai’aduwa, Mashi, Charanchi, Jibiya, Dutsinma, Batsari, Kafur, Sheme, Dandume, Zango, Danja, Bakori, Kaita, Kagadama, da Dankama tun daga ranar Juma’a 17/04/2020.
Haka kuma wannan umurni ya dawo da dakatar da gabatar da Sallar Juma’a a Masallatan mu amma daga ranar Juma’a ta sati mai kamawa. Wannan umurni bai shafi Sallar Juma’ar gobe ba idan Allah Ya kai mu.
Haka kuma an dakatar da gabatar da Tafsirai da Sallar Tarawih da aka saba yi cikin watan Ramadan.
Gidajen Sinima, wuraren kallon Talabijin da kuma na gabatar da tarurruka suma za su kasance a rufe.
Haka kuma Gwamna Aminu Bello Masari ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da takaita shiga da fice a kan Iyakokin wannan jiha.
Gwamnan ya bayyana cewa daukar wannan matakai ya zama wajibi domin kiyaye lafiyar al’umma baki daya.
Wannan bayanai suna kunshe cikin wata takardar da Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa yasa ma hannu. Wannan takarda ta biyo bayan taron dukkanin kwamitocin da suke kula da yaki da wannan kwayar cuta, akwai kuma wakilan Majalisar tsaro ta jiha da kuma limamai da manyan Malamai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.