Home / News / MATSALAR TSARO : DIKKO RADDA YA TAIMAKAWA YAN SINTIRI DA BABURA

MATSALAR TSARO : DIKKO RADDA YA TAIMAKAWA YAN SINTIRI DA BABURA

 

….An Ba Dikko Radda Kyautar Alkur’ani A Rimi

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Dan takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin tutar jam’iyyar APC Dokta Dikko Umar Radda, ya bayar da tallafin kyautar Baburan hawa ga yan kungiyar sintiri na kananan hukumomin Rimi da Kurfi.

Dokta Umar Radda, ya bayyana wannan taimakon Baburan hawan ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan hukda da kafafen yada labarai na kwamitin Yakin neman zaben Gwamnan Jihar Katsina karkashin APC Alhaji Ahmed Abdulkadir, a lokacin da suke kammala zagayen neman kuri’ar jama’a na shiyyar Katsina.

Ya ce, wannan kokarin an yi shi ne da nufin yin yaki da matsalar tsaron da ke addabar yankin.

Dokta Radda, ya bayar da kyautar Babura ne ga kananan hukumomin Rimi da kuma guda uku ga al’ummar mazabar Wurma da ke karamar hukumar Kurfi.

Kamar yadda Alhaji Abdulkadir ya bayyana, Dokta Dikko Umar Radda ya karbi kyautar Alkur’ani da Rago a Fardami, ta karamar hukumar Rimi da kuma Doki wanda mai unguwar Kadandani ya bashi, sai kuma karamar hukumar Rimi ta bashi kyautar Alkur’ani da Takobi daga mai unguwar Tsauri.
Alhaji Ahmed Abdulkadir ya ce dan takarar Gwamnan ya kara jaddada kudirinsa na yin yaki da matsalar tsaro da kuma samawa jama’a aikin yi tare da kara inganta harkokin kiwon lafiya, ya kuma ce zai kara inganta harkokin Noma ta hanyar yin amfani da hanyoyin na zamani a Jihar idan har an zabe shi Gwamna.

 

Hakimin Rimi, Alhaji Aminu Nuhu Abdulkadir tun da farko cewa roko ya yi ga dan takarar Gwamna Dikko Radda da ya tuna da mutanen Rimi da ba su da titi mai kyau, ba ruwan sha,Ba hasken wutar lantarki, idan ya zama zababben Gwamnan Jihar Katsina a tuna da su.

Sai Alhaji Ahmed Abdulkadir ya bayyana a cikin takardar tasa da ya rabawa manema labarai cewa wasu mutane da yawa sun canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda a karamar hukumar Rimi aka samu mutane 1, 500 da suka hada da shugabar mata duk suka koma APC bisa jagorancin tsohon kansila Abdul’Aziz Makwalla.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.