of Campaigning
Ministan yada labarai ya bayyana hakan ne a wajen wani gagarumin taron tattaunawa da kuma fadakar da jama’a da aka yi a garin Kaduna.
Inda ya ce batun gyaran dokokin haraji a Najeriya duk sun dade wanda hakan ya haifarwa da wadansu mutane bin wasu halaye a game da haraji a kasar.
Da yake magana a ranar Asabar a matsayin shugaban taron da hukumar samar da kwararru wajen samar da kyakkyawar dangantaka tsakanin wuraren ayyuka da kuma al’umma (NIPR) a taron da suka shirya na shekarar 2024 da aka yi a Kaduna inda aka Karrama wadansu fitattun mutane a kasa.
Minista Idris ya bayyana cewa samun tattaunawa a tsakanin al’umma a game da abubuwan da suka shafi kasa a matsayin abin da zai taimaka wajen samun hanyoyin ci gaban kasa tare da al’ummarta baki daya.
Saboda haka ne ya tabbatar wa da wannan tsaron da kuma duniya baki daya da cewa wannan batun gyaran dokokin harajin ya dace kowa ya bayar da gudunmawarsa da nufin ciyar da kasa gaba.
Ya kara da bayanin cewa lamarin ba ana yin sa ba ne domin musgunawa ko haifarwa da wani yanki cikas
Gwamnatin Tinubu ba za ta yi abin da zai kawo wa Dimokuradiyya cikas ba. Domin dukkan damar da muka samu a karkashin wannan Gwamnatin duk sun samu ne sakamakon tsarin Dimokuradiyya saboda haka za mu ci gaba da bi tare da tsare dukkan tanaje – tanajen baki daya”, Inji minista.
Idris ya kara jaddada cewa hakika bin hanyar samar da haraji ce abin da ke faruwa a duk fadin duniya baki daya, domin hakan zai ba Gwamnati damar yi wa al’ummarta ayyukan da suka dace
An kuma gabatar da muhimman bayanai da dimbin tattaunawa daga masanan harkokin haraji inda wani da ya zo daga hukumar tara haraji ta kasa ya yi bayanin cewa za a dunkule wadansu dokokin tara harajin ne ta yadda za su bayar da dama ga jama’ar kasa da kuma baki daga wadansu kasashe sukunin samun saukin zuba jari a Najeriya.
Sai dai wadansu da suke tattaunawa a dakin taron sun shaidawa duniya cewa akwai bukatar Gwamnati ta kara duba yanayin dangantakar ta da jama’a domin suk abin da ta fadi ko ta bijiro da shi kowa ya aminta da lamarin musamman ma a bangaren talakawan kasa.
Wadansu manyan malaman addinin Musulunci da kuma na Kirista Shaikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi da kuma Rabaran John Josep Hayab, duk sun yi kira da a kara kula wa sosai wajen fadakar da dimbin al’umma mabiya addinan guda biyu, kasancewar bin hanyar fadakarwa ce babbar hanyar da ya dace a yi wa dimbin al’ummar kasa baki daya domin kwalliya ta biya kudin Sabulu.
An kuma bayar da shawarwarin a shirya irin wannan taron a dukkan Jihohi da kuma yankuna kasa guda shida tare da kowane yankin dan majalisar Dattawa a kowace jiha.