Home / KUNGIYOYI / Muna Bukatar Gwamnati Ta Kara Daukar Matakan Hana Yara Tuki – Mahadi

Muna Bukatar Gwamnati Ta Kara Daukar Matakan Hana Yara Tuki – Mahadi

Mustapha Imrana Abdullahi
An yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin Gwamna Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’I, ta kara himma wajen daukar matakan da suka dace domin daukar tsatstsauran matakin da ya dace ga  masu ba kananan yara tukin Babura masu kafa uku.
Kwamared Mahadi Lawal shugaban kungiyar masu haya da Babura mai kafa uku reshen bakin ruwa cikin garin Kaduna ya yi wannan kiran.
Kwamared Mahadi Lawal ya ci gaba da bayanin cewa su kansu wadanda ke yin wannan sana’ar lamarin da damunsu kwarai su ga karamin yaro na tukin Babur mai kafa uku da sunan daukar fasinja a cikinsa wanda idan aka duba shi kansa yaron bai mallaki hankalin kansa ba da zai iya yin aiki da Babur ba amma sai a bashi ya rika daukar fasinja.
“Wani babban lamari a nan shi ne da zarar an samu nasarar kama irin wadannan yaran masu kananan shekaru sai azo a rika bayar da hakuri daga wadanda suka ba su dukiyar, da wannan ne nake kara yin kira ga Gwamnati da babbar murya da a kara bayar da himma wajen yin maganin wannan matsalar”, inji Mahadi.
Kwamared Mahadi Lawal ya kara da cewa su a matsayin kungiya su na nan a kan kirarinsu wajen taimakawa Gwamnati a kowace fuska kuma a ko wane lokaci domin ganin al’amura sun ta fi dai- dai.
” ko masu kokarin cire sitikar da Gwamnati ta Sanya wa Babura masu kafa uku wanda da su ne ake karbar kudin harajin da ya dace a biya cikin sauki kungiyar na iya bakin kokari wajen samun cimma burin Gwamnati”, Mahadi.
Ya tabbatar da cewa a yanzu sun san inda kudinsu ke tafiya da suke biyan harajin ababen hawan da suke aiki da su, kuma duk wanda ya ya ge wannan alamar karbar haraji to ba shakka za su kama shi su kuma mikawa hukuma shi ko wane ne
Mahadi Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta duba yayan kungiyar wajen sama masu da karin ababen hawa na (Keke – Napep) masu kafa uku domin kungiya ta rabawa masu bukatar yin aiki su dogara da kansu, saboda akwai mutane da yawa su na zaune haka nan babu abin yi.
Kamar dai yadda za a iya gani a cikin wannan hotunan ga kananan yara nan da kungiyar ta kama a yankin bakin ruwa da sunan su na tukin Babura.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.