Home / News / Muna Kira Ga Bola Tinubu Ya Amince Da Bukatar Diezani Allison Madueke – Dokta Suleiman Shinkafi

Muna Kira Ga Bola Tinubu Ya Amince Da Bukatar Diezani Allison Madueke – Dokta Suleiman Shinkafi

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, mai fafutukar kare hakkin bil’adama ne kuma wakilin kare hakkin dan Adam a daukacin yankin nahiyar Afirka wato  (Country representative of African human right defence) ya yi kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da ya duba irin koken da tsohuwar ministar albarkatun Man fetur ta Najeriya Diezani Allison Madueke, ta gabatar gare shi ta hanyar yin amfani da kafafen yada labarai, inda take cewa ta bayar da makudan kudi na miliyoyin dala har Tara (9)  ga Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal tun a lokacin da ya na aiki a matsayin Manajan darakta a  Bankin First Bank domin a ajiye mata.

Amma kuma sai ta yi korafin cewa har ya zuwa yanzu bai yi komai ba domin ganin ya mayar da kudin zuwa ga yan Najeriya.

Kuma kamar yadda Dokta Suleiman Shinkafi ya ce ” sai Diezani ta ci gaba da bayanin cewa Dauda Lawal ya daina ko daukar wayarta ma idan ta kira shi, duk da cewa lauyoyinta, mai gidanta da kuma duk iyalanta duk sun san irin yadda dangantakarsu take da kuma huldarsu da kudin da ta bashi, don haka ne take cewa kudin da duk na yan Najeriya ne kuma kudin da ta dauka ta hanyar da bata dace ba duk ta amince da hakan domin ta fadi hakan don haka ya sabawa kasarta a kan abin da ta aikata game da dibar kudin. Kuma abin da ta yi din ba dai- dai bane domin ta aikata sabanin irin yadda aka amince da ita tare da amince mata aka nada ta ministar albarkatun man fetur ta Najeriya a zamanin mulkin Jonathan, don haka ne take bayani a halin yanzu duk wadanda suka hada kai tare da ita domin aikata wannan cin amana na boye kudin yan Najeriya”

Dokta Shinkafi ya ci gaba da bayanin cewa a kan haka ne muke ganin ya dace a ba ta wannan damar ta dawo Najeriya domin ta Fallasa duk wadanda ta ba kudin, kuma duk wanda aka samu da laifi a hanzarta yi masa hukunci da gaggawa.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ci gaba da cewa ” idan an samu Dauda Lawal da laifin karbar makudan kudi biliyan tara na Dalar Amurka sai kawai a gabatar da shi a gaban kuliya domin fuskantar hukuncin da doka ta tanadar, a hanzarta cire masa rigar kariya da yake da ita a matsayin Gwamna kamar yadda dokar kasa ta tanadar kawai a gabatar da shi a gaban kuliya. Saboda  makudan kudi biliyan tara na Dalar Amurka ba fa kudin Najeriya ake magana ba ko ace miliyan tara a kudin Najeriya, ana magana ne a kudin Najeriya sun wuce tiriliyan Ashirin, haba jama’a in dai har Dauda ya hada kai sun yi hadin baki da wannan matar sun boye wannan kudin ai lamarin ya zama hauka zallah domin kudin ba kadan bane”.

Lallai ya dace Dauda lawal ya fuskanci doka saboda idan a kasashen Asiya ne za su yanke masa hukuncin kisa ne kawai  domin a kasar Cina za su yanke masa hukuncin kisa ne a kasar Koriya ta Arewa ma haka abin yake da kuma kasar Maleshiya da dai dukkan kasashen yankin nahiyar Asiya ai duk za su gabatar da shi ne a gaban jama’a a yanke masa hukuncin kisa domin girman laifin da ya aikata”.

” Sakamakon sace irin wadannan makudan kudade ba wanda zai iya sanin irin dimbin jama’ar da suka mutu sanadiyyar sace kudi irin wannan in har lamarin haka yake. Domin kudin ya dace a samar da ingantacciyar lafiya ga jama’a, samar da kyawawan hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa ga al’umma, amma mutum daya ta hanyar hada kai da wata mata da aka nada ta minista sai gashi an yi wakaci – waka- tashi da makudan kudi irin wannan? da har kudin suka kai biliyan tara na Dalar Amurka ga wani da baya kishin kasa baya kuma kishin Najeriyar baki daya domin indai haka ne baya son yan kasar ko kadan da har yake kiran kansa Gwamnan Jihar Zamfara don haka muke yin kira da lallai ya dace ayi bincike tare da yin hukunci, idan har abin da mu masu rajista kare hakkin bil’adama da kuma muke karantawa a kafafen yada labarai ya zama gaskiya. Idan kuma ba gaskiya bane muna son Gwamna Dauda Lawal ya fito fili ya Karyata maganar domin akwai bata suna da zubar da kimar mutim domin tsohuwar ministar ta yi bayanin komai domin ta fadi har yadda suka hadu ta kuma fadi duk yadda ta bashi kudin kuma ta ce tana da takardun shaidar ta bashi kudin domin lauyoyinta sun sa hannu kuma shima da kansa ya Sanya hannu ya karbi kudin, don haka ne muke ganin idan har shi dan kasa nagari ne ya dace ya dawo da kudin a cikin asusun Gwamnati saboda ya san cewa matar ta gudu ne domin irin yadda ta shiga wani yanayin shari’a sakamakon kwashe kudin kasa ta koma kasar Ingila da zama kuma a yanzu duk ta Gaji baki daya domin abin ya yi mata yawa saboda ko a can ma akwai batutuwa da dama na shari’a a kanta kuma bugu da kari kuma ba ta da lafiya domin ta ce tana fama da cutar ciwon dadi ( Cancer) don haka take son ta dawo gida in lokacin mutuwa ya yi ta mutu a asalin garinsu”.

Hakika wannan abin da ministar ta yi muna cewa ya yi dai – dai amma dai muna yin kira ga fadar shugaban kasa karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ya duba lamarin matar nan ya kuma amince da bukatar ta domin ta dawo gida.

Sabida “akwai dimbin marasa gaskiya da suke take laifinsu da gangan suna kallon laifin wani, ya dace ta dawo domin ta Fallasa duk wadanda ta ba kudi ta yadda doka za ta yi aiki a kansu, mu yan kasa masu kare hakkin bil’adama a madadin dukkan kungiyoyin mu zamu hadu a ranar Albamis a garin Abuja domin yin taron tattaunawa mu fitar da matsaya a bayan taron domin shugaban Najeriya ya duba batun Dawowar tsohuwar ministar cikin Najeriya domin a bayyana duk wadanda suka kwashe kudin kasa da ba a Sani ba amma wasu daga cikinsu suna ta tayar da rijiyar wuya a game da neman kujerun shugabanci da nufin su zama Jagororin jama’a. Kuma zamu nada mutane biyu ko uku da za su ziyarci kasar Ingila domin kaiwa tsohuwar minista Allison Madueke ziyara domin ta ba wannan gagarumar kungiyar kare hakkin dan Adam muhimman takardu da bayanai kuma za a yi hakan ne da zarar an dawo daga hutun sabuwar shekara duk da nufin samun cikakkun bayanai a game da ikirarin da ta yi cewa ta ba Dauda Lawal dalar Amurka biliyan tara domin a ajiye mata lokacin ya na aikin Banki, hakika wannan ba abin yarda bane sam sam da ba wanda zai amince da hakan

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.