Home / KUNGIYOYI / Muna Kira Ga Gwamnati Da Mawadata Su Taimaka A Samu Saukin Sufuri – Aliyu Tanimu Zariya

Muna Kira Ga Gwamnati Da Mawadata Su Taimaka A Samu Saukin Sufuri – Aliyu Tanimu Zariya

Mustapha Imrana Abdullahi
An yi kira ga Gwamnati da kuma mawadata a Jihar Kaduna da su taimaka domin a samu saukin matsalar sufurin da ake fuskanta a Jihar.
Shugaban kungiyar direbobi ta kasa NURTW reshen Jihar Kaduna Alhaji Aliyu Tanimu Zariya ne ya yi wannan kiran lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Alh Aliyu Tanimu Zariya, ya ci gaba da cewa su a matsayinsu na direbobi suna yin iyakar bakin kokarinsu wajen ganin jama’a sun samu sauki musamman ta fuskar sufuri, saboda haka ake ganin ya dace mawadata da kuma Gwamnati su taimaka wajen samar da karin ababen hawa na sufuri domin harkoki su ci gaba da inganta.
Game da batun karin kudin mota da jama’a ke yamadidin cewa an kara a Jihar Kaduna kuwa, sai ya ce ” da jin irin yadda jama’a ke kokawa nan da nan ya nada wani kwamitin da zai zagaya domin tabbatar da me ke faruwa a batun farashin kudin da fasinjoji ke biya, kuma sun zagaya sun kuma kawo rahotonsu cewa ba karin farashin aka yi ba domin idan mutum zai shiga mota misali daga Kawo zuwa kasuwa ba yadda za a ce ya kawo naira dari biyu ko dari da Hamsin, sai dai mafi yawan direbobin sufurin cikin gari idan suka ce ba za su Sabon Tasha ba iyakarsu kasuwa sai aga kamar sun yi wani abu ne daban”.
Ya ci gaba da bayanin cewa ai an kara kudin mai ya kai tashi uku amma ba a kara kudin mota ba, kuma a yanzu duk abin da ake Sayarwa kowa ya san akwai karin kudi, misali abin da acan baya muke sayen tayar mota ta dubu Ashirin da biyu yanzu ta kai dubu Ashirin da Takwas, kuma haka dai lamarin yake a kowa ne fanni farashin ya yi sama”, inji Aliyu Tanimu Zariya.
Saboda haka ne muke ganin ya dace a yabawa irin kokarin da Direbobi ke yi wajen ciyar da kasa gaba da kuma aikin taimakon jama’a baki daya.
Aliyu Tanimu Zariya ya kuma roki Gwamnati da ta duba yuwuwar sayen motocin safa safa da za a yi haya da su ta damka a hannun su domin ayi aiki da su ta yadda al’umma za su amfana.
Sai kuma batun duba yin sassauci a cikin halin da ake ciki game da Baburan hawa na jama’a na kashin kansu da za su yi amfani da shi don hawan mutum daya, ko kai yara makaranta ko asibiti ba wai wadanda za su yi haya ba saboda larura ta yi wa jama’a saukin halin da ake ciki.

About andiya

Check Also

Agriculture: Mrs Tinubu empowers 140 North west women farmers as Gov Idris enhances sustained farmers , women capacity for nation building

By Suleiman Adamu, Sokoto At least , 140 Northwest women farmers in Kebbi state benefitted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.