Home / KUNGIYOYI / MUNA SON GWAMNATI TA KARE MARTABA DA MUTUNCIN AREWA – GAMAYYAR MASU YUNKURI

MUNA SON GWAMNATI TA KARE MARTABA DA MUTUNCIN AREWA – GAMAYYAR MASU YUNKURI

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
An yi kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya da ta kokarta wajen kula da kare martaba da mutuncin kafafen yada labarai da suke a yankin arewacin Najeriya.

Wannan kiran ya fito ne daga gangamin gamayyar masu yunkurin kula da kare martaba da mutuncin yankin arewacin Najeriya masu suna “Arewa Liberation Movement” a lokacin da suka kai ziyarar Sada zumunci a cibiyar yan jarida ta kasa NUJ reshen Jihar Kaduna.
A ta bakin mai magana da yawun wadanda suka kawo ziyarar NASIRU MAMMAN cewa ya yi suna son yin aikin hadin Gwiwa ne tare da kungiyar yan jarida wajen ganin an kwato mutunci da kuma martabar Arewa musamman ta fuskar aikin jarida.
“Zamu fara aikin fadakarwa da wayar da kawunan jama’a da nufin kawar da matsalar bambancin kabila, yare ko addini da wasu ke amfani da shi wajen ciyar da Arewa baya”, inji Nasiru.
Ya ci gaba da cewa su na kalubalantar irin yadda hukumar kula da kafafen yada labarai ta NBC ta hana aiwatar da shirin IDON MIKIYA da aka dade ana fadakar da jama’a a kan al’amuran yau da kullum.
“Muna son fadakar da jama’a ne a game da hadin kai da kokarin wayar da kan jama’a kada su bari wasu su rika yin amfani da addini da kabilanci su raba kawunan jama’a haka kawai, wanda ke ciwa yankin Arewa Tuwo a kwarya”, inji Nasiru.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.