Home / Lafiya / Mutane 318 Ne Suka Kamu Da Cutar Korona A Nijeriya

Mutane 318 Ne Suka Kamu Da Cutar Korona A Nijeriya

Imrana Abdullahi
Bayanai daga hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta kasa ( NCDC) a Nijeriya sun tabbatar da cewa ya zuwa yau ranar Asabar 11 ha watan Afrilu, 2020. Mutane 318 ne suka kamu da cutar Covid – 19 da ake yi wa lakabi da Korona bairus.
Wato an samu karin mutane 13 da suka kamu da Covid – 19 a Nijeriya,Bayanan sun ce akwai mutane 11 daga Legas, 1 daga Kano da 1 daga Jihar Delta.
Sai yawan wadanda aka sallama sakamakon samun lafiya mutum 70 sai wadanda suka mutu sanadiyyar Cutar sun kai 10  saboda haka masu fama da cutar a halin yanzu sun kai 238. Da fatan za a ci gaba da kulawa tare da kiyaye ka’idoji da kuma karin fadakarwa a cikin al’umma.
Kamar dai kuma yadda alkalumman duniya suka tabbatar cewa wadanda suka kamu a duniya sun kai 1,771,483 sai wadanda aka sallama sakamakon samun sauki sun kai 401,464 sai wadanda suka mutane sama da dubu Dari.

About andiya

Check Also

I Want To Assist My People – Barister Abubakar Ahmad Muhammad

FROM IMRANA ABDULLAHI KATSINA All progressive congress (APC) candidate that is hoping to represent Funtua/ …

Leave a Reply

Your email address will not be published.