Home / News / PDP Ta Nada Ahmad Tarika Mataimakin Sakataren Yada Labarai Na Katsina

PDP Ta Nada Ahmad Tarika Mataimakin Sakataren Yada Labarai Na Katsina

 Imrana Abdullahi
A wani lamarin da ke nuna irin gaskiya da aiki tukuru domin ci gaban karamar hukumar Funtuwa,Jihar katsina da kasa baki daya yasa shugabancin Jqm’iyyar PDP reshen Jihar katsina ya tabbatarwa Alhaji Ahmad Tarika da mukami  mataimakin sakataren yada labarai na Jihar Katsina.
Da yake bayyana hakan a kan shafinsa na facebook Dattijo Alhaji Ahmad Tarika ya ce abin da yasa ya Sanya hotonsa lokacin da aka bashi takardar shaidar mataimakin sakataren yada labarai na Jihar Katsina shi ne domin yan uwa masons da yayan PDP su gani domin taya shi murna da kuma yin koyi da irin yadda yake kokarin ci gaban PDP a koda yaushe.
 “Ga yanuwa masoya Na Jamiyar PDP Na Jahar Katsina, Allah da ikon sa Ya bani wani wakilci A jamiyar PDP Na mikamin State Assistant Publicity Secretary, Allah Ya bani ikon sauke wannan nauyin da Allah yabani Ameen Ya Hayyu Ya Kyayum Godiya Nike da duk masoya Allah ya mana Jagora Gaba daya Ameen”, inji Tarika.
Jam’iyyar PDP dai na ta aiwatar da tsare tsaren ganin martaba da kimarta sun dawo a idanun jama’a ta yadda al’umma za su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya domin samun nasarar a dukkan matakai.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.