Home / News / Sanya Mata A Gaba Ne Mafitar PDP – Amina Adamu Soba

Sanya Mata A Gaba Ne Mafitar PDP – Amina Adamu Soba

Imrana Abdullahi Kaduna

 

Hajiya Amina Adamu Soba, tsohuwar yar takara a jam’iyyar PDP ta bayyana cewa matsalar fahimtar Juna ce kawai ke cikin jam’iyyar amma ba sabani ko Rabe Rabe kamar yadda wasu ke kokarin lakabawa yayan PDP ba.

Ta ce hadin kai a zauna ayi shirin zaune da ya fi na tsaye a sasanta.

“Duk bangaren da ake cewa sun rike komai a sasanta su saki wadansu abubuwa domin a cimma nasara a damben naushin da ake bukatar ayi a nan gaba kadan.

Ta bayyana hakan ne a lokacin da take ganawa da manema labarai a ofishin PDP na Jihar Kaduna da ke NDA.

Inda ta ci gaba da cewa ta yaya ana korafin cewa wani bangare ya kama komai ya rike sannan wasu da ake zargi da haka za su yi shiru su kasa daukar mataki, duk da sanin irin babban aikin da ke gaban yayan Jam’iyyar PDP da kasa baki daya domin ganin mulki ya dawo hannun jam’iyyar da za ta taimaki yan Nijeriya wato PDP.

Hajiya Amina Adamu Soba, ta kuma yi bayani a game da irin tasirin mata a lamarin zabe da kuma harkokin siyasa baki day, inda yi kira ga jam’iyyar PDP a kowane irin mataki tun daga sama har kasa da a tabbatar da an jawo mata sakamakon irin tasirin da suke da shi a lokacin zabe.

“Hakika mara su ne ke yin zabe kuma su ne siyasar har ma mulkin baki daya, domin duk Namijin da bai samu komai ba game da nagartar mace a cikin gida ba zai iya gudanar da komai ba a rayuwa koda kuwa ya je zaman ofis ba wani abin da zai gudana, saboda haka mata ba abin a barsu a baya ba ne ga duk mai hankali.

Duk inda aka Sanya Maza uku to a nemo mace ta zama ta hudu, in kuma an sa Maza hudu to a nemo Mata biyu su zama su shida domin a samu tafiyar da aiki kamar yadda ya dace. Mata da ake gani Allah ya ba su basirar hakuri,juriya da hangen nesa saboda mace mai juriya da tunani za ta iya ba Namiji shawarar da shi ba nan ya hango ba kuma idan ya yi aiki da abin zai ga ai nan ne nasarar take, wannan ne nake son jam’iyyar PDP ta gane a dukkan shawarwarinta da rufe Kofar da za ta yi ta tabbatar akwai mata a dukkan al’amuranta baki daya in ana son cimma nasara.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.