Home / News / Sardaunan Badarawa Ya Koma Jam’iyyar APC

Sardaunan Badarawa Ya Koma Jam’iyyar APC

…Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Wanda ya nemi jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a zaben 2023 Honarabul Usman Ibrahim ya fice daga cikin jam’iyyar PDP ya koma PDP.
Honarabul Ibrahim, Sardaunan Badarawa ya yi takara ne a karkashin jam’iyyar PDP domin neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya, ya sanar da ficewarsa ne a ranar 13 ga watan Disamba a cikin wata takardar da ya aikewa shugaban mazabar Badarawa Malali.
Ya ci gaba da cewa “Ya dauki wannan matakin ne bayan samun tattaunawa da tuntuba da ya yi da masu ruwa da tsaki da kuma magoya baya daga dukkan kananan hukumomi guda 7 a mazabar dan majalisar Dattawan Kaduna ta tsakiya a cikin Jihar Kaduna, kafin ficewa saga jam’iyyar PDP zuwa APC da niyyar samun ci gaban da kowa ke bukatarsamu a wannan mazabar, ta Kaduna ta tsakiya da kuma Jihar baki daya”.
Jagoran ya bayyana cewa ya samu kwarin Gwiwa ne daga yan siyasa musamman daga majalisar kasa da kuma wani minista domin ya bayar da dimbin kwarewarsa ga al’ummar da ke can kasa na su rungumi jam’iyyar APC.
Kamar yadda ya ce abin da ya dace ya aiwatar domin biyan bukatun al’ummar Jihar Kaduna shi ne ya shiga jam’iyyar APC tare da Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.