Home / Big News / Shettima Yerima Zai Kawo  Gyara A Yankin Kaduna Ta Tsakiya Da Kasar Baki Daya – Wada Garu

Shettima Yerima Zai Kawo  Gyara A Yankin Kaduna Ta Tsakiya Da Kasar Baki Daya – Wada Garu

Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Wada Garu, ya bayyana gamsuwa da irin yadda aka yi masu kyakkyawar tarba, Lale da marhabin a lokacin da suka je ofishin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna tare da dan takarar su mai neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar neman kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya.
Alhaji Wada Garu, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin taron da ya gudana a ofishin jam’iyyar da ke cikin garin Kaduna, inda ya ce hakika daga zuwansu ofishin jam’iyyar sun ga gagarumin Canji a ofishin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, saboda haka  da ikon Allah za a ga ingantaccen canjin siyasa a yankin mazabar dan majalisar Kaduna ta tsakiya.
“Canjin da muke magana shi ne ya’yan da muka haifa da wadanda aka sanya a gaba mun gano cewa wadansu makiyan ya’yan mu da makiyan wannan yankin Mazabar dan majalisar Kaduna ta tsakiya suna gurbata tunanin ya’yan mu da ba su kayan maye na Wiwi a ba su addauna don haka ne lallai za mu yi yaki da wannan al’amari muna kuma ba kowa shawara da lallai yaki wannan al’amarin. Shugabannin jam’iyya ga kalubale a gare ku duk wanda zai fita kamfe ya dauko yaro ya bashi adda ko Wiwi to, ya soke maganar Takararsa domin ba za mu sanya yayanmu a gaba ba amma mu dauko ya’yan wadansu muna ba su Wiwi a saka su a cikin mota ana horar da su gurbata ciyar hanya ba gaira ba dalili ba.
“NI da na dade a gidan wannan bawan Allah Shettima Yerima Na Sani shi a har kullum idan mun zauna da shi sai ya ce mana wannan al’amarin da muka tsinci kanmu wallahi akwai gyara wadannan yaran da aka haifa lallai akwai gyara a kan mu domin Yakamata mu sanya yaran nan a gurbata ilimi kuma in ma Yaro ba zai yi karatu ba a koya masa sana’a, amma haramun ne, haramun ne ka dauki dan mutum ka bashi Wiwi da Adda ka dauki Kwaya ka mika masa  ka sashi a mota ka ce ya sari wani domin kawai biyan buƙatar ka idan danka ne kai zaka so.
Ina ba kowa shawara cewa duk wanda yazo da irin wannan al’amari ku ce kamar yadda mai girma Gwamna Malam Uba Sani ya ce ne idan mutum zai yi ta’adda a siyasa dansa ya zama shugaba,amma mu zamu yi yaki da wannan al’amarin kuma wannan yankin Kaduna ta tsakiyar da ake magana wallahi kujerar Najeriya ce don haka ba ta yi dai dai da sha sha sha ba, ba ta kuma yi dai dai da wawaye ba, ba ta yi dai dai da Summum-bukumun fahum layarji’un ba.Domin kujera ce mai neman fitacce jajirtacce kamar yadda Sardauna ya zauna a kujerar don haka ina tabbatar maku idan Allah ya yarda a Kaduna ta tsakiya za mu samu maganin Sardauna, kamar yadda Sardauna ya zauna a kujerarsa, Yarima Usman Shettima zai farfaɗo da mutuncin wannan kujerar in Allah yaso.
“Muna rokon ku da ku ba mu dama domin dukkansu ya’yan mu ne amma mu bude idanun mu mu kalli cancantan nan da ake cewa akwai Kalubale a gare mu domin muna da kalubale don haka mu dauki Sabo fil ba mota tsohuwa ba in zaka saya ka samo sabuwa domin ita kwancen mota da ake kira tuwaris daman an ta ba hawan ta, amma idan ka dauki sabuwar mota ka dora ta a kan titi da ikon Allah ba za ta tsaya a hanya ba, kuma ina tabbatar maku cewa ba za mu baku kunya ba zamu daure za mu yi aikin da zamu ci zabe daga sama har kasa da ikon Allah.

About andiya

Check Also

Shettima Yerima Ya Samu Kyakkyawar Tarba, Lale Da Marhabin Daga Shugabannin APC Na Jihar Kaduna

Daga Imrana Abdullahi A ranar Talata ne 22 ga watan Afrilu, dan takarar da ke …

Leave a Reply

Your email address will not be published.