Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen karɓar baƙuncin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, gabanin gudanar da bikin karɓar Gwamna Dauda Lawal a hukumance cikin jam’iyyar mai mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban APC na jihar, Alhaji Tukur Danfulani Maikatako, ne ya sanar da wannan shiri a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar.
A cewarsa, Mataimakin Shugaban Ƙasar zai jagoranci manyan jiga-jigan shugabancin APC na ƙasa zuwa Zamfara a ranar Talata mai zuwa domin halartar wannan muhimmin biki na siyasa, wanda ya biyo bayan sauyin sheƙar Gwamna Lawal zuwa APC—lamarin da ya jawo muhawara a fagen siyasar jihar.
Maikatako ya bayyana jin daɗinsa kan dawowar gwamnan, inda ya jaddada cewa Zamfara na daga cikin jihohin da APC ta daɗe tana da ƙarfi a cikinsu.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal ya taba kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar kafin sauya sheƙarsa a baya.
“Dukkanmu mun san cewa Zamfara jiha ce da APC ke da cikakken karfi tun shekaru da dama, kuma gwamnan da ya dawo ya taba kasancewa sahihin ɗan jam’iyyar,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga dukkan ’ya’yan jam’iyyar a mazabu 147 da ƙananan hukumomi 14 na jihar da su fito ƙwarai domin tarbar Mataimakin Shugaban Ƙasa tare da murnar dawowar gwamnan, yana mai cewa wannan ziyara na da muhimmanci wajen ƙarfafa jam’iyyar gabanin zaɓukan shekarar 2027.
Hakazalika, shugaban jam’iyyar ya gargadi ’ya’yan APC da su guji rikice-rikicen cikin gida, tare da ƙarfafa su su haɗa kai domin cimma muradun siyasa da ci gaban jihar.
A nasa bangaren, tsohon shugaban APC na jihar, Alhaji Lawal M. Liman, ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar da su ƙara zage damtse wajen tara jama’a a matakan mazabu da ƙananan hukumomi, domin tabbatar da cewa APC ta ci gaba da kasancewa tsayayyen dandali na siyasa da ci gaban al’umma.
Ya jaddada cewa haɗin kai da manufa guda ne za su taimaka wajen ƙarfafa jam’iyyar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa ga jihar Zamfara da ƙasa baki ɗaya.
THESHIELD Garkuwa