Home / Labarai / Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Titin Mota Mai Nisan Kilomita 55 A Yobe

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Titin Mota Mai Nisan Kilomita 55 A Yobe

 

Daga Sani Saleh Chinade, Damaturu

 

 

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hanyar motar da tashi daga garin Nguru zuwa garin Gashua- Baymari mai tsawon kilomita 55 tare da mika shi ga gwamnatin Yobe.

Shugaba Buhari wanda Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu ya wakilta, ya ce aikin wani bangare ne na kudirin gwamnatin tarayya na inganta hanyoyin sufuri da bunkasar tattalin arziki a Jihar Yobe da ma kasa baki daya.

 

 

“Kamar yadda kuke gani, muna mika hanyar mai tsawon Kilomita 55, wadda ta hada Nguru-Gashua-Bayamari a Yobe zuwa Jigawa da Borno.”

“Hanyar na da matukar mai mahimmanci wacce ke haɗa al’ummomin iri-iri da ke haɓaka harkokin noma da kasuwanci don sauƙaƙe sufurin kayayyakin gona a tsakanin al’umma.”

 

 

“Ta hanyar haɗa waɗannan al’ummomi tare, wannan hanya ta zama muhimmiyar hanyar sadarwarmu ta kasa,” in ji shi.

Shugaba Buhari ya umarci masu amfani da hanyar da su rika tuka mota kamar yadda doka ta tanada don tattaka hanyar.

 

 

Shi ma a nasa jawabin, Mista Babatunde Fashola, ministan ayyuka da gidaje, ya bayyana cewa ma’aikatar ta fara aikin kashi na farko na kammala ayyuka da mika wa ga hannun gwamnatin Jiha.

 

 

Fashola ya samu wakilcin Mista Celestine Shuwusu, daraktan ma’aikatar, manyan hanyoyin arewa maso gabas a wajen wannan biki na kaddamar da hanyar.

Ya kuma mika godiyarsa ga ma’aikatar kudi da ‘yan majalisar dokoki ta kasa da shugabannin kwamitocin ayyuka na majalisar dattawa da na wakilai a majalisa ta takwas da bada goyon bayan kan wannan aiki.

 

 

Minista Fashola ya kuma yabawa ma’aikatansa da ‘yan kwangila da al’ummomin da abin ya shafa saboda kwazon da suka bayar.

Shi ma da yake nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Alkali, ya ce an fi mayar da hankali ne wajen ganin an hada manyan hanyoyin da suka hada da matatun man fetur, tashoshin jiragen ruwa, manyan makarantu da kuma manyan cibiyoyin kasuwanci.

 

 

Alkali wanda Mista Olusegun Akinmade ya wakilta ya kara da cewa ma’aikatar ta samu nasarar kammala hanyoyi da dama tare da kula da gadoji da dama don tabbatar da cewa masu amfani da hanyar sun samu kwarewa ta hanyar tafiye-tafiye.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Mai Mala Buni ya ce kaddamar da hanyar ya kasance tarihi ga al’ummar jihar bayan shekaru da dama da gwamnatocin da suka gabata suka yi watsi da shi.

 

 

“Muhimmancin wannan hanya ga ci gaban tattalin arzikin jihar ba zai kwatanta ba lura da irin yadda hanyar ta hada wurare da dama na kasar nan har ma da kasar da ke makwabta ka da jihar Yobe Jumhuriyar Nijar”

“Har ila yau, ya zama wata hanyar haɗin kai tsakanin al’umma da kasuwanci tsakanin sauran sassan jihar da al’ummomin kan iyaka na Jamhuriyar Nijar.”

 

 

“Saboda haka, hanyar ita ce hanyar rayuwa ga iyalai da yawa a ciki da wajen jihar,” in ji shi.

Buni ya kara da cewa, tsawon shekaru da dama, harkokin kasuwanci da ci gaban tattalin arzikin wadanda suka dogara da wannan hanya, sun yi kasa a gwiwa sakamakon mummunan halin da take ciki.

Ya kuma godewa gwamnatin shugaba Buhari kan yadda ta kashe makudan kudade wajen kokarin samar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas da Yobe musamman.

 

 

Buni ya kuma mika karin godiyarsa ga majalisar zartaswa ta tarayya bisa mayar da kudaden da gwamnatin Yobe ta kashe na Naira biliyan 18 don sake gina titunan gwamnatin tarayya a jihar da dai sauransu.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.