Home / KUNGIYOYI / Shugabancin NUJ Na Kaduna Ya Gyara Motar Kungiyar Ta Hanyar Hadin Gwiwa

Shugabancin NUJ Na Kaduna Ya Gyara Motar Kungiyar Ta Hanyar Hadin Gwiwa

Wata motar da ta dade da ajiyewa tare da an gyara ta ba kirar Toyota Bas mai cin mutane 14  ta kungiyar yan jarida reshen Jihar Kaduna (NUJ), tuni aka gyara ta bisa jagorancin Asma’u Yawo Halilu.
Aikin gyaran ya tabbata ne tare da hadin Gwiwar kamfanin barasa na Najeriya, da nufin sama wa yayan kungiyar saukin gudanar da ayyukansu na zirga zirga daga nan zuwa can kamar yadda aikin yake.
Da yake gabatar da motar ga shugabannin kungiyar a ranar Alhamis a harabar sakatariyar kungiyar, manaja mai kula da shiyyar Arewa a bangaren samar da kyakkyawar hulda da jama’a Kabiru Kassim ya bayyana kungiyar na NUJ reshen Jihar Kaduna sun dade suna yin huldar arziki tare da kamfanin na tsawon shekaru 50.
” Dalilin gyaran motar an yanke shawarar ne lokacin da aka gudanar da taron tattaunawa tare da mambobin kungiyar a shekarar 2021, nan ne aka cimma yarjejeniyar aiwatar da aikin gyaran motar saboda haka abin da ya faru a yau shi ne kamar mataki ne ya zamo gaskiya”, inji Manajan bangaren hulda da jama’a na kamfanin barasa Kabiru Kassim.
A nata jawabin shugabar kungiyar Hajiya Asma’u Yawo Halilu,godiya ta yi ga kamfanin game da taimakon da suka yi wa kungiyar NUJ na gyaran motar kirar Toyota mai daukar mutane 14 wanda kamar yadda ta ce za a yi amfani da motar ne domin ayyukan mambobin kungiyar.
“Muna yin murna da abin da kamfanin ya yi mana. Saboda haka babu shakka za mu ci gaba da aiki tare da kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Juna wato da kamfanin da kuma kungiyar ta NUJ”, Inji Asma’u.
Shugaban kungiyar yan jaridar, a lokacin da take jawabi, ta tabbatarwa da kamfanin cewa za a ci gaba da kulawa da motar kamar yadda ya dace.
Daga sai Asma’u ta shawarci wadansu kamfanonin kuma da su yi koyi da kamfanin barasa wajen taimakawa kungiyar domin a samu cimma nasarar aiwatar da sauran ayyukan da ke kasa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.