Home / Big News / Shugabannin Kananan Hukumomin Shiyya Ta Daya Sun Tsayar Da Muktar Ramalan Yero Takarar Sanata.

Shugabannin Kananan Hukumomin Shiyya Ta Daya Sun Tsayar Da Muktar Ramalan Yero Takarar Sanata.

 

Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da muke samu daga shiyya ta daya cikin Jihar Kaduna da ke arewacin tarayyar Najeriya na cewa daukacin shugabannin Kananan hukumomin da ke shiyyar karkashin jagorancin Malam Jamilu Albani da ke zaman shugaban karamar hukumar Sabon Gari sun tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Dokta Muktar Ramalan Yero takarar Sanatan yankin.

Bayanan da muka samu sun ce hakan ya faru ne a lokacin wani kwarya kwaryan taron da aka yi a garin Zariya hedkwatar shiyyar ta daya.
Sai dai ana saran a nan gaba kadan ne wanda aka tsayar din zai bayyanawa duniya da kansa,  duk da cewa a wajen wannan taron tuni tsohon Gwamnan ya amince da wannan yunkuri na daukacin shugabannin Kananan hukumomin da ke yankin na shiyyar ta daya, karkashin jagorancin Jamilu Albani.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Kafa Tarihi, Yayin Da Aka Fara Jigilar Alhazai Daga Filin Jirgin Sama Na Gusau

  Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa sabon tarihi bayan da aka gudanar da …

Leave a Reply

Your email address will not be published.